Da 'Dan Gari: Akwai Hannun Masu Mulki da Jami'an Tsaro a Rashin Tsaro, Gwamna

Da 'Dan Gari: Akwai Hannun Masu Mulki da Jami'an Tsaro a Rashin Tsaro, Gwamna

  • Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya bayyana wasu daga dalilan da ya sa har yanzu aka gaza kawo karshen tashin tsaro
  • Gwamnan ya zargi wasu daga cikin jami'an tsaro da jami'an gwamnati da hannu dumu-dumu cikin matsalar tsaron
  • Ya musanta rashin tsaro na da alaka da siyasa, inda ya ce da Naira 500 ma ana shigar da matasa sana'ar satar mutane a Arewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina- Gwamna Umaru Dikko Radda na jihar Katsina ya bayyana dalilin da ya sa rashin tsaro ya ki ci ya ki cinyewa a Arewa.

Gwamnan na Katsina ya yi zargin akwai gurbatattun jami'an tsaro, da jami'an gwamnati da ke cin moriyar tashin hankalin.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya fadi dalilin gwamnonin Arewa na yin taro a Amurka kan tsaro

Gwamna Dikko Radda
Gwamna Dikko Radda ya zargi wasu jami'an gwamnati da mayar da rashin tsaro kasuwanci Hoto Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

A hirar da ya yi da Channels Television, Gwamna Dikko Radda, ya bayyana cewa tuni wadannan gurbatattun jami'ai su ka mayar da abun sana'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ganin illar rashin tsaro

A cewar Gwamnan, wasu gwamnonin Arewa sun halarci taron kan tsaro a kasar Amurka domin karo sani kan yadda za su tunkari matsalar.

Ya ce sun kara fahimtar rashin tsaron ta sabuwar fuska,da samun karin ilimin yadda za su bullowa al'amarin, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Dikko Radda ya kara da cewa ba wai banbancin manufar siyasa ce ke ta'azzara rashin tsaro ba, domin da Naira dari biyar ma ana koyawa mutum satar mutane.

Gwamnan, ya bayyana tafiya kasar Amurka da wasu gwamnonin Arewa su ka yi a matsayin daya daga hanyoyin magance rashin tsaro.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Wannan ziyara ta jawowa gwamnonin suka ganin yadda aka kashe kudi zuwa ketare.

Gwamnatin Katsina ta shirya maganin ta'addanci

A baya kun ji gwamnatin jihar Katsina ta ce ba za ta yi sulhu da yan ta'addan da su ka addabe su ba, domin zai sa 'yan bindigar su raina gwamnati.

Ya ce yin sulhun na raunana ayyukan tabbatar da tsaro, kuma baraka na samuwa, inda ya nuna goyon bayan samar da 'yan sandan jihohi domin dakile rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.