Matawalle: EFCC Ta Yi Magana Kan Binciken Tsohon Gwamnan Zamfara

Matawalle: EFCC Ta Yi Magana Kan Binciken Tsohon Gwamnan Zamfara

  • Hukumar EFCC ta yi magana kan binciken da take yi a kan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle
  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan ta bayyana cewa ba ta rufe binciken da take yi ba a kan ƙaramin ministan na tsaro a gwamnatin Bola Tinubu
  • Muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hukumar ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga wasu mambobin APC da suka yi zanga-zanga a hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bincike kan zargin almundahanar Naira biliyan 70 da ake yi wa Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP tare da sace mawaki a Delta

Ana zargin ƙaramin ministan tsaro ne dai da karkatar da kuɗaɗen lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023.

EFCC ta yi magana kan binciken Matawalle
EFCC ta ce ba ta rufe binciken Bello Matawalle ba Hoto: @BelloMatawalle
Asali: Twitter

EFCC, 'yan AP da Bello Matawalle

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na hukumar EFCC, Wilson Uwajuren ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya faɗi hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zanga a ƙarƙashin ƙungiyar APC Akida waɗanda suka je hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Juma’a.

Masu zanga-zangar dai sun je hukumar ne domin neman a sake buɗe binciken da ake yi kan tsohon gwamnan na jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar Tribune.

Me EFCC ta ce kan binciken Matawalle?

Wilson Uwajuren ya shaida wa masu zanga-zangar cewa da zarar EFCC ta fara bincike ba za a rufe ba, ya kuma ba su tabbacin cewa za a duba buƙatarsu.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kwara ya halarci kotu yayin da EFCC ta gurfanar da kwamishina kan N1.22bn

"Ina so na yabawa mambobin ƙungiyar APC Akida bisa wannan zanga-zangar lumanan. Kuna da ƴancin ku yi zanga-zanga. Kundin tsarin mulki ya ba da ƴancin albarkacin faɗin baki kuma kun yi hakan yau."
"Ina so na ba ku tabbacin cewa EFCC ba ta rufe bincike. Da zarar mun fara bincike, ba mu rufewa. Domin haka ina ba ku tabbacin cewa za mu duba wannan koken na ku. Mun gode sosai."

- Wilson Uwajuren

Matawalle ya caccaki Dattawan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya caccaki ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) kan sukar gwamnatin Bola Tinubu.

Tsohon gwamnan na jhar Zamfara ya bayyana ƙungiyar dattawan da wani ala-ka-kai da ya damu ƴan Arewa, wanda ba ta tsinanawa yankin komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng