ICPC: Kotu Ta Umarci Cafke Sojan da Ya Nemi Takaran Gwamna da Wasu Mutane 2
- Tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya, Usman Jibrin ya shiga matsala bayan umarnin wata babbar kotu a Abuja
- Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin cafke Jibrin da wasu mutane uku kan badakalar makudan kudi har N1.5bn
- Lauyan hukumar ICPC mai yaki da cin hanci, Osuobeni Ekoi Akponimisingha ya shigar da korafi kan mutanen uku
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci cafke tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya.
Kotun ta bukaci a kama Vice Admiral Usman Jibrin mai ritaya da wasu mutane biyu kan badakalar makudan kudi har N1.5bn.
Hukuncin kotun a shari'a Jibrin v ICPC
An bukaci a cafke Usman Jibrin wanda ya yi takarar gwamnan jihar Kogi a zaben bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai Shari'a, Inyang Ekwo shi ya ba da wannan umarni a yau Juma'a 3 ga watan Mayu a Abuja, cewar Leadership.
Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ita ta gurfanar da mutanen uku a gaban kotu kan almundahana da makudan kudi.
Kotun ta ba da umarnin cafke mutanen bayan karbar korafi mai lamba FHC/ABJ/CR/158/2023 daga lauyan hukumar mai suna Osuobeni Ekoi Akponimisingha, cewar Nairametrics.
Zargin da ICPC ke yi wa Usman Jibrin
Lauyan ya gurfanar da Usman Jibrin Oyibe da Adam Imam Yusuf da Burgediya-janar Ishaya Gangum Bauka.
Ana zargin mutanen da ba da bayanan karya ga kamfanoni da suke da hannun jari a ciki.
Kamfanonin sun hada da Lahab integrated da Multi Services Limited da Gate Coast Properties International Limited da Ummays Hummayd Energy Ltd.
Kotu ta dakatar da karin kudin wuta
A wani labarin, kun ji cewa wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano dakatar da hukumar kula da hasken wutar lantarki ta kasa, (NERC) daga karbar sabon farashin kudin wutar daga kwastominsa a jihar.
Kotun ta kuma haramtawa kamfanin rarraba hasken wuta (KEDCO) ci gaba da karbar sabon farashin kudin wutar a yankunan da suke.
Wannan na zuwa ne bayan kara kudin wuta da kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya (NERC) ta yi a kwanakin baya wanda ya harzuka jama'a.
Asali: Legit.ng