Tallafin N50,000: Gwamnati Ta Yi Karin Haske, Ta Fadi Lokacin Cigaba da Biyan Kudi

Tallafin N50,000: Gwamnati Ta Yi Karin Haske, Ta Fadi Lokacin Cigaba da Biyan Kudi

  • Yayin da wasu suka fara samun tallafin N50,000, ma'aikatar masana'antu da kasuwanci ta yi karin haske kan tallafin
  • Ma'aikatar ta ce mutane 1m daya ne kadai za su samu tallafin daga miliyan 3.6 da suka nemi tallafin a fadin kasar
  • Wannan na zuwa ne bayan fara biyan tallafin ga wandansu da aka tantance inda ma'aikatar ta ce za a ci gaba da biya a karshe wata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan mutanen da za su samu tallafin N50,000 da ake bayarwa ga 'yan ƙasar.

Gwamnatin ta bakin ma'aikatar kasuwanci ta ce mutane 1m ne kawai za su ci gajiyar daga cikin mutane miliyan 3.6 da suka nemi tallafin.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Gwamnati ta yi karin haske kan ci gaba da biyan tallafin N50,000
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirinta kan ci gaba da biyan tallafin N50,000. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe aka fara cike tallafin N50,000?

Tallafin da aka fara cikewa a ranar 9 ga watan Maris na wannan shekararta 2024 zai ba 'yan Najeriya N50,000 ba tare da sun biya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tallafin kudin zai taimaka wurin bunkasa kananan sana'o'i a kananana hukumomi 774 da ke fadin Najeriya, cewar Nairametrics.

Mata da matasa za su kwashi 70% yayin da masu bukata ta musamman zasu tashi da 10%, cewar rahoton Punch.

Yaushe za a ci gaba da biyan tallafin?

"Ba da kudin ba wai kan wani tsari ya ke ba, sai dai duk wadanda aka tantance."
"Muhimmin abin shi ne tallafawa mutane 1,290 a kowace karamar hukuma a Najeriya wanda zai kai mutane miliyan daya."
"Ba da lamunin kuma ya danganta da tantance lambar NIN bayan saka lambar BVN, ana zaben mutanen ne ba tare da wani son rai ba."

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

- Ma'aikatar kasuwanci da masana'antu

Tuni aka rufe cike neman tallafin inda ma'aikatar ta ce za a ci gaba da biyan kudin a karshen watan Mayu da muke ciki.

Kayan abinci sun fara sauka a Najeriya

A wani labarin, an fara murna bayan tabbatar da cewa kayan abinci musamman hatsi sun fara sauka a kasuwanni a wasu jihohi.

Dillalan kayan abincin a jihohin Arewacin Najeriya da suka hada da Gombe da Bauchi da Jigawa ne suka tabbatar da haka a wannan makon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.