Kaya Na Iya Kara Tsada Sakamakon Wani Canjin Farashin Dalar da Kwastam Tayi

Kaya Na Iya Kara Tsada Sakamakon Wani Canjin Farashin Dalar da Kwastam Tayi

  • Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) ta canza lissafin da ta ke amfani da shi wajen karbar kudin shigo da kaya daga kasashen ketare
  • A maimakon N1,373.64/$1 da Kwastam ta bayar a ranar 1 ga Mayu, hukumar ta canza farashin Dala zuwa N1,441.58 a ranar Juma'a, 3 ga Mayu
  • Muda Yusuf, jami’i a cibiyar tallata kamfanoni masu zaman kansu (CPPE), ya ce irin wannan sauyin na Kwastam na da illa ga tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar hana fasa kwauri ta kasa (NCS) ta yi karin farashin canjin kudaden waje na shigo da kaya zuwa N1,441.58 kan kowacce dala.

Kwastam ta daidaita kudin shigo da kaya zuwa N1,441/$1
Kwastam ta daidaita kudin shigo da kaya, ana fargaba kayan za su yi tsada a kasuwa. Hoto: @CustomsNG
Asali: Twitter

Kwastam ta canza kudin shigo da kaya

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Kotun Kano ta dakatar da karbar sabon kudin wutar lantarki

Wannan ya nuna karuwar kashi 4.94% idan aka kwatanta da N1,373.64/$1 da hukumar ta bayar a ranar 1 ga Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lura da wannan karin da hukumar kwastam ta amince da shi a ranar Juma'a a kan shafin kasuwanci na gwamnatin tarayya.

Yawancin hukumar kwastam tana amfani da farashin canji da Babban Bankin Najeriya (CBN) a wajen saka kudin shigo da kaya da kuma lura da cinikin kudin a kasuwar canji ta duniya.

Sai dai an lura cewa farashin Kwastam ya fi farashin gwamnati na N1,402/$1 da aka yi kasuwancin kudin a ranar 2 ga Mayu.

CBN ya gargadi Kwastam kan canjin kudi

A cewar CBN a ranar 23 ga watan Fabrairu, hukumar kwastam da sauran bangarorin da ke da alaka da ita dole ne su rika amfani da farashin da take bayarwa wajen saka harajin shigo da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

Babban bankin ya ce ya kamata a yi amfani da farashin da ta bayar a kudin shigo da kaya domin tantance harajin da za a kakabawa kayayyakin, jaridar The Cable ta ruwaito.

Muda Yusuf, babban jami’in gudanarwa na cibiyar tallata kamfanoni masu zaman kansu (CPPE), ya ce irin wannan sauyin na Kwastam na da illa ga tattalin arziki.

Gwamnati ta magantu kan sabon albashi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ranar 1 ga watan Mayu a matsayin ranar da sabon albashin ma'aikatan Najeriya zai fara aiki.

A cewar karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha, gwamnati za ta aiwatar da karin duk da cewa kwamitin karin albashin bai kammala aikin da aka ba shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.