Gwamnati Ta Yi Alkawari Na 2 a Jere a Kan Matsalar Ruwa a Jihar Gombe

Gwamnati Ta Yi Alkawari Na 2 a Jere a Kan Matsalar Ruwa a Jihar Gombe

  • Kwamishinan ruwa na Gombe, Muhammad Saidu Fawu ya yi alkawarin samar da ruwa a jihar zuwa ranar Asabar mai zuwa
  • Kwamishinan ya yi jawabin ne a yau Juma'a yayin da yake hira da ƴan jarida kan matsalar ruwa da ta adabi mutanen jihar
  • Alkawarin na zuwa ne bayan gwamnan jihar ya yi alkawarin cewa zai shawo lamarin zuwa ranar Laraba da ta gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Kwamishinan ruwa na jihar Gombe, Muhammad Saidu Fawu ya bada hakuri ga mutanen jihar kan cigaba da wahalar ruwa da suke fama da ita.

Layin ruwa a Gombe
Gwamnatin Gombe ta yi alkawarin magance matsalar ruwa zuwa ranar Asabar. Hoto: Shuaibu Salisu El-Diouf
Asali: Facebook

Kwamishinan ya bada hakuri ne tare da tabbatar da cewa zuwa ranar Asabar za a shawo kan matsalar.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Kano suka yi wawason 'yan daba sama da 3000 a shekara 1

Tashin farashin ruwa a Gombe

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa farashin ruwa ya tashi a Gombe sakamakon karancinsa a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashin farashin ya kara saka al'umma cikin wahala yayin da wasu marasa galihu ke amfani da ruwa marar tsafta.

Daga ina matsalar ruwa ta faro?

A yau Juma'a kwamishinan ya tabbatar da cewa matsalar ta faru ne sakamakon faduwar wayoyin wutar lantarki guda 31.

A cewarsa, wa wayoyin ne suka hada Gombe da Dadinkowa, wanda anan ne ake hako ruwan da ake samarwa jihar.

Amma ya ce a halin yanzu ma'aikata suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da komai ya dawo daidai cikin kankanin lokaci.

Saboda haka ne ma kwamishinan ya yi alƙawari ga mutanen jihar kan cewa ruwan zai dawo ranar Asabar.

Ya kara da cewa mutane sai sun kara da hakuri da yi wa gwamnati uzuri tare da tuna cewa aikin ba karami ba ne.

Kara karanta wannan

Lamari ya lalace; Gwamantin jihar Kano ta saka dokar ta baci a kan harkar ilimi

Rashin ruwa ya yi kamari a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadau Inuwa Yahaya ya yi alkawarin magance matsalolin da suka dabaibaye harkar samar da ruwan sha a jihar.

Gwamna ya yi alkawarin ne ranar Talata bayan matsalar ruwa ta yi ƙamari a fadin jihar sakamakon rashin wuta, ya kuma bayyana cewa ranar Laraba, 1 ga watan Mayu komai zai kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng