Yadda Ake Rijista: Rundunar Sojin Najeriya ta Sanar da Daukar Sababbin Sojoji a 2024

Yadda Ake Rijista: Rundunar Sojin Najeriya ta Sanar da Daukar Sababbin Sojoji a 2024

  • A ranar Juma'a, 3 ga watan Mayu, rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin ma'aikata a shekarar 2024
  • A cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani, rundunar ta bayyana yadda za a nemi aikin da kuma abubuwan da ake bukata
  • Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, rundunar sojin Najeriya ta na kokarin kara ma'aikata domin dakile matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu, rundunar sojin Najeriya ta shaida wa ‘yan Najeriya masu sha’awar shiga aikin soja cewa za ta fara daukar ma'aikata 'yan bataliya ta 87.

Rundunar wadanda ke da kwalin kammala sakandare ne kawai za su nemi aikin.

An bude kofar shiga aikin sojan Najeriya na shekarar 2024
Rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin sojoji a bataliya ta 87. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Ranar farawa da rufe neman sojoji

Kara karanta wannan

An kama shugaban ‘yan bindigar da ake zargin sun farmaki jirgin kasan Abuja-Kaduna

Legit Hausa ta tattaro daga shafin rundunar na X cewa masu sha'awar aikin sojan za su fara cike bayanansu a yanar gizo daga ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta kuma bayyana cewa za ta rufe cike bayanan a ranar Juma’a 7 ga watan Yuni, 2024.

Shafin yanar gizon rundunar da za a nema aikin shi ne recruitment.army.mil.ng kuma neman shiga aikin sojojin Najeriya kyauta ne.

An tattaro cewa wadanda suka tsallake matakin fako za su je tantancewar da za a yi a jihohi wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 20 ga watan Yuni zuwa 3 ga Yuli, 2024.

Karin bayanin hanyar cika aikin soja

Rundunar har ila yau, ta bada yadda za a cike aikin cikin sauki ba tare da wata matsala ba.

1. Ka shiga yanar gizo kamar haka recruitment.army.mil.ng domin cike bayanai.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

2. Sannan za ka cike dukkanin takardu da kuma bayanai da ake bukata kamar haka:

i. Fasfo

ii. Takardun makaranta

iii. Ka/ki kace mai shekara 18 zuwa 22

iv. Shaidar kasancewa dan jiha

v. Takardar haihuwa

vi. Lambar NIN da BVN

Sojoji sun dakile hari a Taraba

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa dakarun sojoji sun samu nasarar dakile wani hari da 'yan bindiga suka yi yunkurin kaiwa kauyen Kweserti da ke Ussa, jihar Taraba.

A yayin dakile harin ne sojojin suka yi nasarar kashe 'yan bindiga biyu tare da kwato makamai da harsasai yayin da 'yan ta'addan suka tsere.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.