Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga

Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga

Tuni aka soma cike gurbin samun aiki a rundunar sojin Nigeria a zangon shekarar 2020, kuma Legit.ng Hausa ta tattara bayanai na yadda za a shiga cikin aikin sojin.

A ranar Laraba, rundunar sojin Nigeria ta bude shafinta na daukar aiki da ke yanar gizo, domin daukar sabbin ma'aikata a matakin DSSC26/202 da kuma SSC47/2021.

DSSC26/202 sune wadanda zasu shiga aikin a bangaren hukumar soji da suka samu gajeren horo na kai tsaye, yayin da SSC47/2021 zasu shiga a bangaren hukumar soji da suka samu gajeren horo na musamman.

Shelkwatar rundunar sojin ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, tana mai cewa nan take ne za a fara cike gurbin aikin, kuma kyauta ne.

"Muna sanar da masu sha'awar shiga aikin soji a matakin SSC47/2021 da DSSC26/2021, da su sani mun bude shafin cike gurbin aiki, za a fara nan take," a cewar rundunar sojin.

Ga hanyoyin da zaka bi domin cike gurbin aikin soji a 2020.

KARANTA WANNAN: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun sace mutane 5

Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga
Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga
Source: Twitter

Da farko ka shiga shafin daukar aiki na rundunar da ke a yanar gizo recruitment.army.mil.ng ko ka ziyarci babba shafin rundunar sojin kai tsaye.

Ka zabi bangaren aikin da kake so.

Ka dora dukkanin takardunka kamar hoto, takardun kammala karatu, takardar haihuwa ko rantsuwar shekaru, takardar asalin jiha, takardar shaidar zama mamban wata cibiya.

A yayin kammala rejistar, ana so masu sha'awar aikin su sauke shaidar yin rijistar a takarda.

Ana son wani magatakardar kotun shari'a ya sa hannu a fejin farko na shaidar yin rejistar da aka saukar, yayin da shugaban karamar hukuma zai sa hannu ko wani babban jami'in soji, a matakin Laftanal Kanal, zai sa hannu a feji na biyu na takardar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel