Wasu 'Yan Jam’iyyar APC Sun Yi Kira Ga EFCC Kan Cigaba da Binciken Ministan Tinubu
- Kungiyar APC akida ta yi kira ga hukuma mai yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa kan binciken ministan tsaro na tarayya
- Shugaban kungiyar ne, Malam Musa Mahmud ya bayyana kudurin nasu bayan zanga-zanga a hedikwatar EFFC da ke Abuja
- Kungiyar ta kuma bayyana alfanu da Najeriya za ta samu idan EFCC ta yi halin maza wurin cigaba da binciken Belolo Matawalle
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kungiyar APC akida ta yi kira ga hukuma mai yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa kan cigaba da binciken ministan tsaro, Bello Matawalle.
'Yan APC sun je hedikwatar EFCC
Kungiyar ta ce babu wani dalili da zai sa hukumar ta dakata da binciken ministan saboda yana cikin gwamnati mai-ci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa 'yan kungiyar sun isar da sakon ne ga hukumar EFCC bayan gudanar da zanga-zanga a hedikwatar ta dake Abuja.
Yayin da suke gudanar da zanga-zangar, sun ce amincewa da yadda EFCC ke gudanar da ayyukanta ne ya ba su karfin gwiwar gabatar da korafin nasu.
Jawabin shugaban APC akida a EFCC
Shugaban kungiyar, Musa Mahmud ya ce ya kamata hukumar EFCC ta bude sabon shafin binciken tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.
A cewar shugaban, sun yi kiran ne a wannan lokacin kasancewar gwamnatin APC ta dauki matakai masu tsauri kan jami'an gwamnati da aka samu da cin hanci da rashawa.
Malam Musa Mahmud ya bada misalin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a kan yadda gwamnatin Bola Tinubu ta nuna ba sani ba sabo ga wadanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.
Zargin da ake yi wa Bello Matawalle
Idan ba a manta ba dai tun ranar 18 ga watan Mayu na 2023 ne aka ji EFCC ta fara binciken ministan kan karkatar da kudi naira biliyan 70.
Ana zargin tsohon gwamna Bello Matawalle da karkatar da kudin ne bayan gwamnatin jihar ta karbo su a matsayin lamuni daga wani banki.
'Yan kungiyar sun ce suna kiran ne a matsayinsu na masu biyayya ga jam'iyyar da kuma kare martabar ta, cewar jaridar the Nation.
Sun ce idan har EFCC ta amsa kiran to hakan zai zama izina ga sauran 'yan baya masu rike da madafun iko wurin kaucewa cin dukiyar al'umma.
EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello
A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban Alkali ranar Talata.
EFCC ta ce an samu nasar gurfanar da shi ne ta hannun lauyansa, Abdulwahab Muhammad kuma kotun ta daga sauraren karan zuwa 10 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng