Gaba da Gabanta: Kotun Kano ta Dakatar da Karbar Sabon Kudin Wutar Lantarki

Gaba da Gabanta: Kotun Kano ta Dakatar da Karbar Sabon Kudin Wutar Lantarki

  • Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da kamfanin rarraba hasken wuta na KEDCO daga karbar sabon farashin kudin wuta a hannun abokan huldarsa
  • Haka kuma an dakatar da hukumar kula da hasken wutar lantarki ta NERC daga nemi kwastomomi su biya sabon karin da aka yi a watannin baya
  • Sabon karin da aka yi ya shafi kwastomomin da ke amfana da hasken wuta na kusan awanni 20 a tsarin band A da B a fadin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Wata babbar kotu da ke zamanta a jihar Kano dakatar da hukumar kula da hasken wutar lantarki ta kasa, (NERC) daga karbar sabon farashin kudin wutar daga kwastominsa a jihar.

Kara karanta wannan

Kaya na iya kara tsada sakamakon wani canjin kudin da Kwastam tayi

Kotun ta kuma haramtawa kamfanin rarraba hasken wuta (KEDCO) ci gaba da karbar sabon farashin kudin wutar.

kotu ta dakatar da karin farashin wuta a Kano
Wata kotu a Kano ta dakatar da KEDCO da NERC daga karbar sabon kudin wuta Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa hukuncin ya shafi dukkanin abokan hulɗar kamfanin da ke tsarin band A da B, kamar yadda gwamnati ta ce su aka karawa kudin wutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lantarki: Kamfanoni sun shigar da kara

Tun da farko, wasu jerin kamfanoni ne su ka nemi kotun karkashin Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ta hana kamfanin KEDCO tilasta musu biyan sabon kudin wuta.

Kamfanoni sun hada da Supper Sack Limited, BBY Sack Limited, Mama Sannu Industries Limited, Dala Good Nigeria, Tofa Textile and Manufacturers Association of Nigeria.

Kotun ta amsa rokon kamfanonin, tare da dakatar da kamfanin KEDCO daga tilasta musu ko cin zarafinsu kan sabon kudin wutar har sai an kammala sauraron shari'ar, kamar yadda Leadership News ta wallafa.

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

Kotun ta yi umarnin wallafa dakatarwar a jaridu, sannan ta sanya ranar 16 ga Mayu domin ci gaba da sauraren karar.

Karancin Wuta: Minista ya shawarci 'yan Najeriya

Mun ruwaito muku cewa ministan wutar makamashi, Adebayo Adelabu ya shawarci 'yan Najeriya da ka da su kuskura su biya sabon kudin wuta idan ba su sha wutar da aka yi musu alkawari ba.

Ya fadi haka ne lokacin da ya bayyana gaban Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki a Abuja, inda ya ce bai wajaba kan 'yan Najeriya su biya sabon farashi ba idan babu wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel