Wike: Minista Ya Sake Jawo Kasar Turai Domin Samar da Tsaro a Abuja

Wike: Minista Ya Sake Jawo Kasar Turai Domin Samar da Tsaro a Abuja

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana kudurin neman haɗaka da kasar Hungary domin inganta harkokin tsaro da noma
  • Mista Nyesom Wike ya yi jawabin ne yayin da ya kai wata ziyara ofishin jakadancin kasar Hungary da ke birnin tarayya Abuja
  • Jakadan kasar ta Hungary, Endre Peter Dere ya bayyana cewa a shirye suke wurin hada kai da Najeriya domin samar da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana aniyarsa na yin hadaka da kasar Hungary a fannin tsaro da noma.

Nyesom Wike
Ministan Abuja ya nemi kasar Hungary ta sayarwa Najeriya makamai domin inganta tsaro. Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

A cewar ministan, yunkurin da suka yin yana daga cikin bada muhimmanci da gwamnatin Bola Tinubu ta yi wurin samar da cikakken tsaro a Abuja.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fayyace abin da ya tilastawa Tinubu cire tallafin man fetur

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa Mista Wike ya bayyana kudurin ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin jakadancin kasar Hungary dake Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Najeriya ke bukata daga Hungary?

A lokacin ziyarar, ministan ya bayyana abubuwan da gwamnatin ke buƙata daga kasar Hungary domin dakile barazar tsaro a Abuja.

Ya lissafa bukatar samun jirage marasa matuka da za su rika samar da cikakken tsaro a birnin tarayyar.

Amma sai dai ya ce akwai bukatar a tantance irin jiragen da za su dace da birnin domin kaucewa ɓacin rana da kuma kasancewarsu ingantattu.

Mista Wike ya kara da cewa lalle akwai matsalar tsaro a Abuja amma da yardar Allah za su magance ta idan suka samu hadakar.

Jawabin Nyesom Wike kan harkar noma

A bangaren noma kuwa, ministan ya tabbatarwa jakadan a kan cewa lalle suna shirye wurin yin haɗaka.

Kara karanta wannan

Yayin da ake ta zarge zarge, Kashim ya kare gwamnatin Buhari, ya fadi tsare tsaren Tinubu

Ya ce gwamnatin Najeriya za ta bada filayen noma ga kasar Hungary ta inda dukkan ƙasashen za su ci moriyar juna, cewar Premium Times

Jawabin jakadan Hungary

Jakadan kasar Hungary a Najeriya, Endre Peter Dere ya yabawa ministan bisa bajinta da ya nuna a birnin tarayyar a cikin kankanin lokaci.

Kuma ya ce lalle kasar Hungary za ta bada gudumawa ga Najeriya wurin magance matsalolin tsaro musamman ta hanyar sayar mata da jirage marasa matuka.

Shugaban kasa ya gana da hafsoshin tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi ganawar sirri da hafsoshin tsaro a fadar shugaban kasa

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai mai ba da shawara a kan harkokin tsaron kasar, Malam Nuhu Ribadu

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng