Gwamnan CBN Ya Bayyana Abubuwan da Ke Kawo Tashin Farashin Kayayyaki a Yanzu

Gwamnan CBN Ya Bayyana Abubuwan da Ke Kawo Tashin Farashin Kayayyaki a Yanzu

  • Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana sababbin hanyoyin da suke kawo hauhawar farashin kayayyaki
  • Olayemi Cardoso ya ce lalle akwai bukatar masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki su yi tsayuwar daka wurin magance matsalolin
  • Masana tattalin arziki sun bayyana hanyoyin da za a bi wajen ganin an yi nasara wurin yaki da tashin farashin kayayyaki a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya bayyana abubuwan da suke kawo hauhawar farashin kayan masarufi.

CBN governor
Babban bankin Najeriya ya bayyana ababen da ke jawo tashin farashi domin daukan mataki. Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hanyoyin ne domin hukumomin da suke ƙoƙarin daidaita farashin kaya su samu damar shawo kan lamarin.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa shugaban bankin ya lissafa karin farashin makamashi a cikin abubuwan da suke jawo tashin farashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fayyace abin da ya tilastawa Tinubu cire tallafin man fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin abubuwan da suka kawo tashin farashi

Amma a cewarsa an kara samun sababbin abubuwan da suke kara jawo tashin farashi ta bangaren masu sayar da kaya da masu saya.

Ya lissafa sayan abinci mai yawa da gwamnatoci suka yi domin raba tallafi a matsayin sabon dalilin da ya jawo tashin farashi, cewar Nairametrics.

Ya kuma ce sayan kayan abinci mai yawa da ake a lokacin bukukuwa kamar azumi da sauransu suna jawo tashin farashin kayan masarufi.

Tashin Farashi: Mafita daga masana tattali

Mista Cardoso ya ce yafi dacewa ga hukumomi masu kula da harkokin kudi su magance sababbin hanyoyin domin samar da mafita a kan abin da ya shafi daidaita farashi.

Wani masanin harkokin kudi, Emem Usoro ya bayyana hanyoyin da ya kamata a bi wurin magance tashin matsalar.

Ya ce dole a dauki matakin kawo karshen matsalar kamar magance matsalolin farashin kaya lokacin bukukuwa.

Kara karanta wannan

Karin Albashi: Kungiyar TUC ta ba 'yan Najeriya tabbaci kan hauhawan farashin kaya, ta fadi dalilai

Ya kuma kara da cewa akwai buƙatar zama cikin shirin ko-ta-kwana domin dakile matsalar tashin farashi da za ta iya faruwa a gaba.

Emefiele ya shiga tsaka mai wuya

A wani rahoton, kun ji cewa Babbar Kotun tarayya ta ba wa tsohon Gwamnan CBN wa'adi ya bayyana a gabanta kan wasu makudan kuɗaɗe da aka ciyo bashi

Hakan ya biyo bayan rashin ganin Emefiele a zaman kotun na ranar Talata amma lauyansa ya bada uzuri

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng