Kano: An Tsinci Gawar Dalibar Jami’ar Aliko Dangote a Dakin Kwananta

Kano: An Tsinci Gawar Dalibar Jami’ar Aliko Dangote a Dakin Kwananta

  • Rahotanni sun nuna cewa an tsinci Aisha Yahaya, wata dalibar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, jihar Kano
  • An ce dalibar ta rasu ne jim kadan bayan rubuta jarrabawarta ta farko a jarabawar kammala zangon karatu na farko na jami'ar
  • Hukumar jami'ar da kuma kungiyar dalibai musulmi sun mika sakon ta'aziyya ga iyalai, 'yan uwa da dalibai kan mutuwar Aisha

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - An tsinci gawar wata dalibar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Aisha Yahaya, a wani gidan dalibai da ke wajen makarantar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tsinci Aisha, 'yar aji 300 a fannin kimiya da fasahar abinci jim kadan bayan ta koma dakinta.

Kara karanta wannan

Fatima Alkali: Ɗalibar da ta rikita Arewa bayan ta yi kacal kaca da jarabawar UTME

Dalibar jami'ar Aliko Dagote da ke Kano ta rigamu gidan gaskiya
Kano: An tsinci gawar dalibar aji 3 a jami’ar Aliko Dangote jim kadan bayan zana jarabawa. Hoto: Aliko Dangote University Of Science and Technology - Adustech Wudil
Asali: Facebook

An ce dalibar ta rubuta jarrabawarta ta farko a jarabawar kammala zangon karatu na farko da ake kan gudanarwa a jami’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin abokan karatunta sun danganta mutuwar dalibar da takurawa kai wajen karatu da fargabar jarrabawa.

"Aisha daliba ce mai hazaka" - ADUSTECH

A cikin wasikar ta’aziyya, hukumar jami’ar ADUSTECH ta bayyana matukar bakin cikinta dangane da rasuwar Aisha Yahaya.

Sanarwar ta ce:

"Aisha ba daliba ce mai hazaka ba kwai, ta kasance mai sanyin zuciya. Za a rika tunawa da ita a kan sha’awarta da sadaukarwarta ga karatu”.

Jami’ar ta kara da cewa, abin da ya sa mutuwarta ta girgiza mutane shi ne sanin cewa Aisha ba ta fama da wata rashin lafiya har zuwa ajalinta.

MSSN ta yi ta'aziyyar rasuwar dalibar

Wani dalibin makarantar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa jaridar PUNCH Metro cewa:

Kara karanta wannan

"Ba talakawa kadai ba ne", Dangote ya koka kan illar da karyewar Naira ya yi masa

“An tsinci gawar ta jim kadan bayan ta gama zana jarabawarta ta farko. Wasu na kusa da dalibar sun ce watakila ta mutu ne sakamakon zafin kai na jarabawar da zana.

A halin da ake ciki, kungiyar dalibai musulmi ta Nijeriya, ta fitar da sakon ta'aziyya wadda Ameer, Haruna Haruna, da jami’in hulda da jama’a na 1, Ibrahim Tata suka sanya wa hannu.

An tsinci gawar dalibar UNIPORT

A wani labarin makamancin wannan, Legit Hausa ta ruwaito yadda aka tsinci gawar wata dalibar jami'ar Fatakawal a dakin kwananta da ke a wajen makaranta.

Shugabar sashen kula da dalibai na jami'ar, Chima Wokocha, ta ce an samu kwalbar maganin kwari kusa da gawar yarinyar wanda ya sa ake fargabar ta dauki ranta ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.