Kungiyar Kwadago Ta Koka Kan Yadda Borno Ke Biyan ’Yan Fansho N4,000 a Wata
- Kungiyar kwadago ta NLC a jihar Borno sun koka kan yadda har yanzu gwamnatin jihar ke biyan wasu tsofaffin ma'aikata N4,000 a wata
- Shugaban NLC na jihar, Yusuf Inuwa wanda ya bayyana hakan ya roki Gwamna Babagana Zulum da ya sake duba kudaden 'yan fansho
- Kungiyar ta kuma jinjinawa gwamnatin jihar Borno kan bullo da shirin Blue Ocean wanda a cewarta yana taimakawa ma'aikata a jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Borno - Ma’aikatan jihar Borno a ranar Laraba sun yi korafin cewa har yanzu wasu da suka yi ritaya a jihar suna karbar Naira 4,000 a wata a matsayin fansho.
“A halin da ake ciki akwai ‘yan fansho da har yanzu suke karbar Naira 4,000 a matsayin fansho duk wata.”
- A cewar shugaban kungiyar kwadago reshen jihar, Yusuf Inuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amfanin shirin Blue Ocean ga ma'aikata
Jaridar The Punch ta ce Inuwa bai ambaci adadin wadannan ‘yan fanshon ba amma ya roki Gwamna Babagana Zulum da ya sake duba kudaden 'yan fansho na jihar.
Inuwa ya godewa gwamnatin jihar kan shirin kasuwanci da ta yi mai taken Blue Ocean Market, wanda a cewarsa, zai kawo ci gaba mai yawa a jihar.
Shugaban NLC ya kuma ce shirin ya samar da damarmaki masu yawa ga ma’aikata a Borno, jaridar Vanguard ta ruwaito.
NLC ta jinjinawa kokarin Zulum
Inuwa ya ce:
“A karkashin shirin Blue Ocean, gwamnatin jihar Borno ta samar da motocin bas domin jigilar jama’a a farashi mai rahusa, wanda su ma ma’aikata ke mora a halin yanzu.”
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Inuwa ya zayyana wasu abubuwa da gwamnati ta yi wa ma’aikata da suka hada da aiwatar da biyan kudaden karin girma ga ma’aikata.
Sauran sun hada da biyan N1bn ga iyalan ma’aikata da ‘yan fansho da suka mutu; da kuma biyan N500m na giratuti ga ma'aikatan kananan hukumomi da sauransu.
Gwamnati ta aiwatar da sabon albashi
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta aiwatar da sabon albashin ma'aikata a ranar 1 ga watan Mayu, 2024.
A cewar karamar ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da karin albashin duk da kwamitin albashin bai gabatar da rahotonsa ba.
Asali: Legit.ng