Hukumar Hisba Ta Fara Shirye Shiryen Auren Zawarawa Karo Na 2 a Mulkin Abba
- Hukumar Hisba ta jihar Kano ta fara shirye shiryen auren zawarawa karo na biyu a mulkin Abba Kabir Yusuf
- Kwamandan rundunar ne, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana lamarin yayin hira da manema labarai
- Sheikh Daurawa ya kuma bayyana cewa a wannan karon akwai kudirin shigo da kwararru domin su mori shirin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya fara bayani kan yadda auren zawarawa na gaba zai gudana a jihar.
Sheikh Aminu Daurawa ya fara bayanin ne a jiya Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai.
A cewar rahoton jaridar Leadership, Sheikh Daurawa ya ce wannan karon auren zai hada da bangarori da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bangarorin da za su amfana da auren kwamandan ya lissafa da 'yan jarida inda yace za a basu gurbi guda 50.
Ya kuma kara da cewa akwai wasu bangarorin ma'aikata da za su shiga cikin wadanda za su ci moriyar shirin.
Sababbin wadanda za a shigo dasu shirin
Yayin da yake zantawar, Sheikh Daurawa ya bayyana irin nasarorin da auren da ya gabata ya haifar a jihar, inda aka daura aure 1,800.
A cewarsa, saboda nasarar da auren ya haifar ne ma suke shirin shigo da wasu bangarorin domin su ma a dama da su.
Ya ce bayan 'yan jarida, za a shigo da alkalai, lauyoyi da ma'aikatan lafiya a sassa daban-daban na jihar, cewar Tribune Online
Dalilin kirkiro auren zawarawa
Yayin da yake bayyana dalilan yin auren, malamin ya ce an kirkiro gudanar da bikin ne domin rage alfasha tsakanin mutane tare da kare martabarsu.
Ya kuma ce shigo da kwararru a bangare daban-daban zai kara wa shirin armashi da karɓuwa a cikin al'umma.
Sai dai kuma har ya kammala hirar, malamin bai ambaci hakikanin ranar da za a daura auren ba.
An daura auren zawarawa a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan uwa da abokan arziƙi ne suka halarci babban Masallacin Kano domin shaida auren zawarawa da 'yan mata 1,800
Kwankwaso ne wakilin Anguna yayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kasance waliyyin amare kuma gwamnatin Kano ta ɗauki nauyi
Asali: Legit.ng