'Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 3 da Ke Ikrarin Su Jami’an EFCC Ne

'Yan Sanda Sun Kwamushe Mutum 3 da Ke Ikrarin Su Jami’an EFCC Ne

  • Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kama jami'an bogi masu damfara da fashi da makami a jihar Nasarawa
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ramhan Nansel ne ya bada sanarwar ga manema labarai jim kaɗan bayan kama su
  • Ya kuma bayyana irin artabun da suka yi kafin samun nasarar da kuma bayyana irin aikin barna da bata-garin suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta sanar da cafke mutane guda uku da ke ƙaryar cewa su jami'an hukumar EFCC ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da kama su ga manema labarai.

Kara karanta wannan

"Ba talakawa kadai ba ne", Dangote ya koka kan illar da karyewar Naira ya yi masa

Nigerian Police
Yan sanda sun kama sojojin bogi a jihar Nasarawa. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Rahoton Tribune Online ya tabbatar da cewa a ranar 17 ga watan Afrilu 'yan sanda suka samu korafi a kan mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen masu amfani da koriyar mota sun damfari daliban kwalejin kimiyya da fasaha da ke Nasarawa kuma sun kama wani dalibi mai suna Adudu Kingsley.

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan, daga lokacin da labarin ya riske su suka tsananta bincike kan kamo bata-garin.

Yadda aka kama sojojin bogin

A farkon lokacin da 'yan sanda suka far musu, bata-garin sun yi dabara sun sulale. Amma sai suka kira jami'an su da ke Anguwar Madugu ta wayar tarho domin su sha kansu.

A yayin da suke tserewa 'yan sandan sai jama'a suka afka musu da duka harda jikkata daya daga cikinsu.

Daga nan 'yan sanda suka dauke su zuwa asibiti kuma a nan ne wanda aka jikkata din ya mutu, cewar The Guardian Nigeria

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su a Arewacin Najeriya

Daga nan ne sai 'yan sanda suka dauki matar jami'an bogin zuwa ofishinsu domin zurfafa bincike.

Bayan bincike sai 'yan sanda suka samu bayanan sirri na sauran da suka gudun kuma hakan ya jawo nasarar kamo su.

Sojojin bogin sun amsa laifi

Mutane ukun da aka kama sun amsa laifin su na ayyukan damfara da fashi da makami a yankunan Keffi da Nasarawa.

An kuma samu waɗanda suka zalunta da dama da suka bayyana a ofishin 'yan sanda domin a bi musu kadunsu.

EFCC ta gufanar da kwamishina a jihar Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Kwara a gaban kotu

Hukumar EFCC na tuhumar Ademola Banu da karkatar da N1.22bn a lokacin da yake riƙe da wannan muƙamin a jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng