'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban PDP Tare da Sace Mawaki a Delta

'Yan Bindiga Sun Hallaka Tsohon Shugaban PDP Tare da Sace Mawaki a Delta

  • Ƴan bindiga sun aikata sabon ta'addanci a jihar Delta bayan sun hallaka wani tsohon shugaban jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Ika ta Kudu
  • Tsagerun sun farmake shi ne a cikin gonarsa tare da yin yunƙurin garkuwa da shi, wanda bayan sun kasa samun nasara sai suka hallaka shi
  • Wani mawaƙi a jihar ya faɗa hannun masu garkuwa da mutane inda suka buƙaci a biya su Dala 200,000 kafin su sako shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - An kashe tsohon shugaban jam’iyyar PDP na mazaɓa ta 10 a Abavo, ƙaramar hukumar Ika ta Kudu a jihar Delta, Elder Francis Amamosa.

An kuma yi garkuwa da wani mawaƙi mai suna Goodnews Emuemu, wanda aka fi sani da Gnewzy a jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fara shirin yin waje da wasu ministocinsa kafin cika shekara 1 a mulki

'Yan bindiga hallaka tsohon shugaban PDP
'Yan bindiga sun sace mawaki a jihar Delta Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Wasu ƴan bindiga da ke sanye da kayan ƴan sanda ne suka yi garkuwa da Gnewzy a hanyar Eklat da ke yankin Ughelli a jihar, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda kashe tsohon shugaban PDP

Wata majiya daga iyalan Francis da ya tabbatar da kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban na PDP, ya yi zargin cewa makiyaya ne suka aikata wannan aika-aikar.

Ya ce sun farmasa ne a gonarsa tare da yunƙurin yin garkuwa da shi tare da wasu manoma guda biyu, cewar rahoton jaridar Vanguard.

A kalamansa:

"Ya bijirewa masu garkuwa da mutanen tare da ƙalubalantar tsaurin idonsu na shigowa har cikin gonarsa domin yin garkuwa da shi. Nan take kawai sai suka harbe shi."
"Amma da suka gano cewa harsasan sun gaza shiga jikinsa sai suka yi amfani da adduna wajen ji masa raunukan da suka yi sanadiyyar mutuwarsa."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai kazamin hari a wurin zaman makoki, sun kashe bayin Allah

Ya ƙara da cewa makiyayan sun yi awon gaba da wasu manoma biyu da ke kusa da wajen.

'Yn bindiga buƙaci kuɗin fansa

A halin da ake ciki, manajan mawaƙin, Obas9ice, wanda shi ma yana cikin motar lokacin da maharan suka farmake su, ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane sun tuntuɓe shi

Ya bayyana cewa miyagun mutanen sun nemi kuɗin fansa Dala 200,000 a cikin kwanaki bakwai.

Ƴan bindiga sun kai sabon hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a garin Maradun da ke jihar Zamfara wanda nan ne mahaifar ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

A yayin harin da ƴan bindigan suka kai, sun salwantar da rayukan mutum biyu tare da yin awon gaba da aƙalla mutum 30 zuwa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng