Karin Kudin Lantarki: Majalisar Wakilai Ta Ba Hukumar NERC Sabon Umarni

Karin Kudin Lantarki: Majalisar Wakilai Ta Ba Hukumar NERC Sabon Umarni

  • Majalisar wakilai, a zamanta na yau Talata ta nemi hukumar wutar lantarki ta Najeriya NERC da ta janye batun karin kudin wuta
  • Majalisar ta dauki matakin ne bayan amincewa da wani kudiri mai muhimmanci ga jama'a da Hon. Nkemkanma Kama ya gabatar
  • Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga Afrilu, NERC ta amince da ƙarin kudin wutar lantarki ga abokan ciniki dake a ƙarƙashin 'Band A'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci hukumar kula da samar da wutar lantarki ta Najeriya NERC da ta dakatar da aiwatar da sabon kudin wutar da ta sanar a baya.

Majalisar ta dauki matakin ne a yayin zaman majalisar a ranar Talata, bayan amincewa da wani kudiri mai muhimmanci ga jama'a,

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya mamaye PDP, shugabannin jam'iyya sun dakatar da dan majalisar tarayya

Majalisar wakilai ta dakatar da gwamnati daga karin kudin wutar lantarki
Majalisar wakilai ta nemi hukumar NERC ta dakatar da shirin aiwatar da karin kudin wuta. Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Hukumar NERC ta yi karin kudin lantarki

Nkemkanma Kama, dan majalisar wakilai na jam’iyyar Labour Party (LP) daga jihar Ebonyi ne ya dauki nauyin wannan kudiri, jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kama ya ce kudurin na neman magance muhimman batutuwan da suka shafi karin kudin wutar da aka yi ba zato ba tsammani a Najeriya.

Yadda aka tashin kudin shan wutar lantarki

A ranar 3 ga Afrilu, NERC ta amince da ƙarin farashin wutar lantarki ga abokan ciniki dake a ƙarƙashin rukunin samun wutar na 'Band A'.

Hukumar ta ce wadanda ke karkashin wannan rukunin da ke samun wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kullum, za su fara biyan Naira 225 a kan kowace kilowatt (kW), daga ranar 3 ga Afrilu.

Gwamnati ta kare karin kudin lantarki

Da yake kare karin kudin a gaban kwamitin majalisar dattawa a ranar Litinin, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnati ba za ta iya biyan tallafin lantarki ba.

Kara karanta wannan

'Idan dai babu wuta, babu biyan sabon kudin lantarki', Minista ya zuga 'yan Najeriya

Jaridar The Cable ta ruwaito Adelabu ya ce domin a farfado da fannin, akwai bukatar gwamnati ta kashe kusan dala biliyan 10 a duk shekara nan da shekaru 10 masu zuwa.

Adelabu ya ce a yanzu masu zuba jari suna nuna sha’awarsu a fannin wutar lantarki saboda karin kudin wutar lantarki ga abokan huldar na 'Band A'.

Gwamnati za ta siyar da DisCos

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito gwamnatin tarayya ta sha alwashin sayar da kamfanonin rarraba wutar lantarki guda biyar (DisCos) na kasar.

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ce za a kammala siyar da kamfanonin rarraba wutar lantarkin a cikin watanni uku ga wadanda aka san suna da karfin kula da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.