"Ka Ci Amanarsu": Jigon PDP Ya Dira Kan Tinubu Game da El Rufai da Yahaya Bello, Ya Fadi Dalilai
- Yayin da tsoffin gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi ke cikin wani hali, jigon PDP ya yi martani kan abin da ya faru da su
- Segun Showunmi ya ce Shugaba Bola Tinubu ya ci amanar Nasir El-Rufai da kuma Yahaya Bello bayan wahalar da suka sha
- Ya ce ya kamata Tinubu ya saka baki yayin da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da tsohon gwamnan Kaduna a matsayin Minista
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Jigon jami'yyar PDP, Segun Showunmi ya magantu kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya yaudari na hannun damansa.
Showunmi ya nuna takaici musamman kan yadda shugaban ya ci amanar Nasir El-Rufai da Yahaya Bello duk da wahalar da suka sha masa.
Zargin jigon PDP kan Tinubu
Jigon PDP ya bayyana haka a shafinsa a X inda ya ce da saks hannun Tinubu a dukkan matsalolin da tsoffin gwamnonin biyu ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zai yi wahala Majalisar Dattawa ta ƙi tantance El-Rufai a matsayin Minista idan da Bola Tinubu ya shiga lamarin.
"Yarbawa sun dauki cin amana a kansu kamar yadda ake cewa muna amfani da mutum idan muka samu biyan buƙata kuma mu watsar shi."
- Segun Showunmi
"El-Rufai da Bello sun bautu" inji Sowunmi
"Kamar Tinubu bai damu da abubuwan da za su faru ko za su biyo baya ba."
"Ku duba yanzu halin da El-Rufai ya ke ciki duk da irin goyon bayan da ya ba Shugaba Tinubu a zabe."
"Yanzu ga Yahaya Bello yadda yi yaki kamar mahaukaci saboda Tinubu ya yi nasara a Kogi."
- Segun Showunmi
Segun ya ce yadda Yahaya Bello ya yi Tinubu da dukkan karfinsa har kyashi ya ke idan ya kwantanta da lalatacciyar jami'yyarsa ta PDP.
Yesufu ta magantu kan El-Rufai da Bello
A wani labarin, 'yar gwagwarmaya a Najeriya, Aisha Yesufu ta magantu kan halin da Nasir El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki a yanzu.
Aisha ta ce wannan ya kamata ya zama izina ga sauran 'yan siyasa cewa mulki ba zai tabbata a hannunsu ba.
Ta ce 'yan siyasar Najeriya sun dauki shekaru takwas kamar za su tabbata inda suke cin karensu babu babbaka.
Asali: Legit.ng