An Gano Dalilan da Suka Sanya Darajar Naira Ta Yi Kasa Kan Dalar Amurka
- Darajar Naira ta yi faɗuwar da ba a taɓa ganin irin ta ba a cikin sati ɗaya tun daga watan Fabrairun shekarar 2024 da muke ciki
- A makon da ya gabata, darajar Naira ta faɗi ƙasa warwas da kaso 23% a kasuwa kan kuɗin Amurka watau Dala
- Dalilai biyu ne suka taimaka wajen faɗuwar darajar Naira ciki har da wayon da bankuna suka riƙa yi domin samun riba sosai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Darajar kuɗin Najeriya watau Naira ta ragu da kaso 23% a cikin kwana huɗu a satin da ya gabata.
Wannan faɗuwar da darajar Naira ta yi kan Dalar Amurka ba a taɓa ganin irinsa ba tun watan Fabrairun 2024.
Ana neman Dala a kasuwa
Ƙaruwar neman Dala a kasuwannin bayan fage da bankuna da gazawar bankin CBN wajen ba ƴan canji Dala a kan lokaci, ya jawo darajarta ta faɗi a satin da ya gabata, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, a ranar Juma'a bankin CBN ya kawowa Naira ɗauki, inda darajarta ta farfaɗo a kasuwar bayan fage.
Tun da CBN ya dawo siyarwa da ƴan canji Dala, farashin bayan fage bai kai na banki ba.
Misali a ranar Juma'a, 19 ga watan Afirilu farashin N1,120 kan Dala ɗaya bai kai na banki ba da kaso 64.5% wanda yake a N1,234.49 kan Dala a wannan ranar.
Meyasa Naira ta faɗi ƙasa kan Dala?
Domin amfani da wannan damar, bankuna sai suka koma siya a kasuwannin bayan fage, za su siya Dala a arha sannan su siyar da ita da tsada ga abokan cinikinsu.
Da yake tabbatar da hakan, shugaban ƙungiyar ƴan canji watau BDCs, Dakta Aminu Gwadabe, ya bayyana cewa:
"Dalilai biyu ne suka sanya darajar Naira ta faɗi ƙasa. Na farko shi ne mutane suna siya a kasuwar bayan fage, sai su sanya a asusunsu na Dala daga nan su siyar a banki."
"Suna yin hakan ne saboda farashin kasuwannin fage bai kai na banki ba. Dalili na biyu kuma shi ne dawowar P2P."
"Bayan an kulle Binance, wasu kamfanonin kuma sai suka faso. Irinsu Binance za su samu riba ne kawai idan darajar Naira ta faɗi saboda kasuwa ce da zaka siya da arha ka siyar da tsada."
Ƙoƙarin CBN wajen farfado da Naira
A wani labarin kuma, kun ji cewa bankin CBN ya ce yana yin duk mai yiwuwa domin ganin an samu daidaiton farashin Naira a kasuwar hada-hadar kudade (FX).
Shugaban bankin kasar, Olayemi Cardoso ya ce ana ƙoƙarin ganin an samu farashi mai kyau da za a rika musayar Naira da shi.
Asali: Legit.ng