Murna Yayin da Hafsan Tsaron Najeriya Ya Laluɓo Hanyar Daƙile Matsalar Tsaro, Ya Fadi Dalilai

Murna Yayin da Hafsan Tsaron Najeriya Ya Laluɓo Hanyar Daƙile Matsalar Tsaro, Ya Fadi Dalilai

  • Yayin da ake fama da matsalar tsaron a Najeriya, hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa ya samo mafita
  • Janar Musa ya bayyana cewa hadin kai tsakanin al'ummar Najeriya ne kadai zai dakile matsalar tsaro da ta'addanci a ƙasar
  • Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cikin wani hali na matsalar tsaro a fadin kasar baki daya musamman a yankin Arewa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana hanyar dakile matsalar tsaro da ta'addanci.

Janar Musa ya ce hadin kai shi ne babban maganin matsalar tsaro da ta'addanci a Najeriya, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Ana murna sauƙi ya fara samuwa, Tinubu ya sake tsoratar da 'yan Najeriya, ya yi jan ido

Hafsan tsaro ya gano hanyar dakile matsalar tsaro a Najeriya
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya fadi hangar dakile matsalar tsaro. Hoto: @kc_journalist.
Asali: Twitter

Wace hanya aka samo na dakile tsaro?

Hafsan tsaron ya bayyana haka a jiya Asabar 27 ga watan Afrilu a birnin Abuja yayin taron tsoffin dalibai na makarantar USOSA.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Muna cikin matsala a Najeriya, ya kamata mu hada kai domin tabbatar da dakile matsalolin tsaro."
"Wannan taro zai kara tabbatar mana da cewa hadin kai ya na da muhimmanci wurin kawo karshen matsalolinmu."
"A rayuwa dole za mu rinka cin karo da matsaloli, zamu fadi amma kuma dole mu ci gaba da tunkarar gaba, dole 'yan Najeriya mu hada kai domin tabbatar da dakile matsalolinmu."

- Christopher Musa

Ya bukaci hadin kai da kishin ƙasa

Musa ya ce akwai bukatar 'yan kasar su rika jin kasar a jikinsu domin tabbatar da hadin kai a kasar, cewar Arise News.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke fama da matsalolin tsaro kama daga fashin daji da garkuwa da mutane da kuma ta'addanci.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Tinubu ya magantu kan halin kunci

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya magantu kan halin kunci da 'yan kasar ke ciki a Najeriya.

Shugaban ya ce tabbas ya san 'yan Najeriya suna cikin halin kunci saboda matakan da ya ke dauka a kokarin kawo sauyi.

Tinubu ya ce ba zai gajiya ba wurin ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai ko da kuwa za a sha wahala na lokaci guda idan za a samu abin da ake nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.