“Zargin Gobara”: Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji 243 Ya Yi Saukar Gaggawa a Legas

“Zargin Gobara”: Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji 243 Ya Yi Saukar Gaggawa a Legas

  • Wani jirgin Air Peace da ya ɗauko fasinjoji da dama ya samu tangardar na'ura jim kadan bayan ya fara shirin sauka filin jirgin Legas
  • An ruwaito cewa jirgin wanda ya taso daga Fatakwal, babban birnin Ribas ya yi saukar gaggawa bisa zargin gobara ta tashi a wutsiyar jirgin
  • Sai dai Air Peace a sanarwar da ya fitar ya ce na'ura ce kawai ta nuna alamar tashin wutar amma ba gaskiya bane, kuma jirgin ya sauka lafiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jirgin Air Peace da ya taso daga Fatakwal ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Alhamis.

Air Peace ya yi magana kan jirginsa da ya samu tangardar na'ura
Jirgin Air Peace ɗauke da fasinjoji 243 ya yi saukar gaggawa a Legas. Hoto: Air Peace / Getty Images
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jirgin Dana Air ya kwace yayin da ya sauka a tashar jirgin ta Legas, wanda ya jawo aka dakatar da ayyukansa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana fargabar wasu sun rasu bayan gini ya rufto musu a Kano

Jirgi: "Tangardar na'ura aka samu" - Air Peace

Kamar yadda kamfanin jiragen Air Peace ya sanar a shafinsa na Twitter, lamarin ya faru ne bayan matukin jirgin ya ga alamar tashin gobara a wutsiyar jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

"Muna so mu sanar da jama'a cewa mun gamu da wata tangarda a jirgin mu da ya tashi daga Fatakwal zuwa Legas a ranar 25 ga watan Afrilu, 2024.
"Yan mintuna kafin jirgin ya sauka, matukinmu ya lura da alamar tashin gobara a wutsiyar jirgin. Matukin ya dauki dukkanin matakan kariya tare da magance matsalar."

Jirgin na dauke da mutane 255

Sanarwar kamfanin ta nuna cewa tangardar na'ura ne kawai aka samu amma babu wata gobara da ta tashi a wutsiyar jirgin.

"Matukin jirgin ya yi gaggawar sanar da cibiyar kula da tafiye-tafiyen jiragenmu da ke Legas halin da ake ciki misalin karfe 5:37 na yamma."

Kara karanta wannan

FAAN ta dauki matakin gaggawa da gobara ta tashi a filin jirgin saman Legas

- A cewar sanarwar.

Jirgin mai dauke da fasinjoji 243 da ma'aikata 12 an ce ya sauka lafiya a kan titin 18L na filin jirgin saman Legas, rahoton Channels TV.

Gobara ta tashi a filin jiragen Legas

A jiya Alhamis, 25 ga watan Afrilu, Legit Hausa ta ruwaito cewa gobara ta tashi a wani bangare na filin jiragen saman Murtala Muhammad da ke Legas.

An tattaro cewa hukumar gudanarwar filin jirgin ta dakatar da ayyukanin dukkanin jiragen sama a bangaren yayin da hukumar kashe gobara ta kai dauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.