EFCC Ta Sanar da Ranar Gurfanar da Hadi Sirika Bisa Zargin Satar Naira Biliyan 8
- Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana lokacin da za ta gurfanar da tsohon minista, Hadi Sirika
- Tsohon ministan sufurin jiragen saman ya kwana biyu yana ganawa da masu binciken hukumar a hedikwatar ta da ke Abuja
- Hukumar ta yi bayanai ma su muhimmanci a kan adadin kudin da ake zargin shi da batarwa wanda hakan ne ya tsawaita binciken
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Yayin da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya shafe kwana biyu a garkame hannun hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) an sanya lokacin gurfanar da shi.
EFCC: Zargin da ake yi wa Hadi Sirika
HKama shi ya biyo bayan binciken da hukumar EFCC ke yi ne bisa salwantar da kudi da aka yi a kan samar da jiragen Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta ruwaito cewa jami'an hukumar sun ce a halin yanzu ba za su yi magana da 'yan jarida a bayyane ba a kan lamarin.
Amma kuma sun tabbatar da suna da masaniya a kan abin da ke faruwa da tsohon ministan a hukumar tasu.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa har yanzu hukumar EFCC tana bincike a kan lamarin domin gano hakikanin kudin da aka kashe wurin samar da jiragen.
Kuma a cewar majiyar, har yanzu tsohon ministan ya na hedikwatar hukumar da ke Abuja ya na amsa tambayoyi a kan badakalar
Yaushe za a gurfanar da Hadi Sirika?
Sun kara tabbatar da cewa a mako mai zuwa ne za a gurfanar da Hadi Sirika a gaban kotu domin ya amsa tuhumar da ake mi shi ta sace kudi sama da naira biliyan 80.
Ana zargin Hadi Sirika ne da kan yadda ma'aikatarsa ta bayar da kwangilar bogi ga wasu kamfanoni wanda daya daga ciki mallakar dan uwan sa ne Abubakar Sirika.
Hukumar EFCC ta tsare Hadi Sirika
A wani rahoton kuma, kun ji cewa Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon ministan Muhammadu Buhari, Hadi Sirika.
EFCC ta kama shi ne bisa zargin sa da hannu cikin badakallar kudi sama da naira biliyan takwas a lokacin da yake minista
Asali: Legit.ng