Ganduje Ya Kaddamar da Titin ‘Abdullahi Ganduje’ da Aka Gina a Wajen Kano

Ganduje Ya Kaddamar da Titin ‘Abdullahi Ganduje’ da Aka Gina a Wajen Kano

  • Gwamnatin jihar Gombe karkashin jagorancin Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ta kaddamar da titi mai sunan Abdullahi Umar Ganduje
  • Shugaban jam'iyyar APC ta kasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin kaddamar da titin da kansa a tsakiyar makon nan
  • Legit ta tattauna da wani dan jam'iyyar APC a jihar Gombe domin jin irin tasirin da ziyarar za ta yi a kan zaben da za a gudanar a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gombe - Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da titin da aka sanya wa sunan sa a jihar Gombe.

Ganduje road
Gwamnatin jihar Gombe ta kaddamar da hanya mai sunan Ganduje. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Asali: Facebook

Yayin da shugaban jam'iyyar ya ziyarci jihar Gombe domin ayyukan da suka shafi zaben kananan hukumomi, gwamna jihar ya karrama shi da sanya wa titi sunan sa.

Kara karanta wannan

APC: Ana tangal tangal da kujerarsa, Ganduje ya fadi wadanda za su iya gyara Najeriya

Yadda titin Ganduje yake a Gombe

Cikin sanarwar da mai taimakawa gwamnan Gombe a kan yada labarai Isma'ila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook, ya nuna cewa titin mai tsawon kilomita 1.6 ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin ya kuma kara da bayyana cewa hanyar ta haɗa wurare masu muhimmanci a cikin karamar hukumar Gombe da karamar hukumar Akko.

Wuraren da hanyar ta haɗa ya kunshi GRA, Nayinawa, Bagadaza, Kuwait da hanyar ratse ta bayan gari wanda dukkan su wurare ne da ake hada-hada.

Ganduje ya yi wa gwamnatin Gombe godiya

Lokacin da yake kaddamar da titin, Dakta Ganduje ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa ayyukan cigaba da yake kawowa jihar.

Ya kuma kara nuna godiya ga gwamnan bisa karrama shi da yayi da sanya wa titin sunan sa tare da kira ga al'ummar jihar da su cigaba da goyon bayan gwamnan.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Shugaban jam'iyyar ya kuma aika sakon shugaba Bola Tinubu ga gwamnan inda ya ce lalle shugaban kasan yana jin labarin yadda gwamnatin jihar ke ayyukan cigaba kuma yana alfahari da hakan.

'Yan APC sun yi murna da zuwan Ganduje Gombe

Legit ta yi hira da wani dan jam'iyyar APC, Aminu Isa, a kan zuwan shugaban jam'iyyar na kasa jihar Gombe kuma ya bayyana yadda suka ji da zuwan nasa.

A cewar Aminu, Ganduje ya zo ne domin karfafa yan takararsu a zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar ya kuma ce kwalliya ta biya kudin sabulu.

Ya ce zuwan Ganduje zai sanyaya gwiwar 'yan jam'iyyar adawa ta yadda za su cire rai a zaben da za a gudanar, kuma hakan ta tabbata.

Jam'iyyar APC ta goyi bayan Ganduje

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar APC na jihohi sun kaɗa kuri'ar amincewa da Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Jagororin sun tabbatar da wannan matsaya ne yayin da suka ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Talata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng