Yahaya Bello: An Gargadi Tinubu Ya Dauki Mataki Kan EFCC Game da Tsohon Gwamna

Yahaya Bello: An Gargadi Tinubu Ya Dauki Mataki Kan EFCC Game da Tsohon Gwamna

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan zargin Yahaya Bello da EFCC take yi, an shawarci Shugaba Bola Tinubu kan lamarin
  • Kungiyar gamayyar jam'iyyu ta UPPP ta shawarci Tinubu da ya ja kunnen hukumar EFCC kan zargin tsohon gwamnan
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar EFCC ke zargin tsohon gwamnan da badakalar N84bn yayin da ya ke mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gamayyar jam'iyyun siyasa ta UPPP reshen jihar Kogi ta ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan dambarwar Yahaya Bello.

Kungiyar ta bukaci Tinubu ya ja kunnen hukumar EFCC game da yadda ta ke gudanar da bincikenta kan tsohon gwamnan Kogi.

Kara karanta wannan

Ganduje ya kaddamar da titin 'Abdullahi Ganduje' da aka gina a wajen Kano

An shawarci Tinubu kan gargadin EFCC game da binciken Yahaya Bello
Kungiyar UPPP ya ba Bola Tinubu shawara kan gargadin EFCC game da Yahaya Bello. Hoto: @officialEFCC, @OfficialGYBKogi/X).
Asali: Twitter

Shawarar ƙungiyar UNPP ga Tinubu kan EFCC

Yayin tattaunawa da manema labarai, Ibrahim Itodo ya ce ya kamata hukumar ta yi hankali kan binciken tare da bin dokar kasa, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Itodo ya ce bai kamata shugaban hukumar ya dage kan zargin Yahaya Bello ba wurin rufa-rufa kan rashin yin katabus yayin da ya ke jagorantar hukumar.

Ya bukaci shugaban hukumar ya yi murabus tun da ya gaza tabuka wani abu na kirki a hukumar ba tare da sauke fushinsa kan Yahaya Bello ba.

An bukaci cire sunan Yahaya Bello daga zargi

"Mun yi mamaki martanin Sufetan 'yan sanda da ministan shari'a da sauran jami'an tsaro na ayyana Yahaya Bello ana nemansa ruwa a jallo."
"Wannan tsantsan rashin bin dokar kasa ne da kuma biris da kundin tsarin mulkin Najeriya da ke bamu kariya."

Kara karanta wannan

JAMB: Mahaifin da ya rubutawa yaronsa jarabawar UTME 2024 ya shiga hannun hukuma

"Muna ba da shawarar ayi gaggawar cire sunan Yahaya Bello daga cikin wadanda ake nema ruwa a jallo saboda an yi hakan ne kan rashin bin doka da kuma tsari."

- Ibrahim Itodo

Ododo ya raba Yahaya Bello da EFCC

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya yi karfin hali inda ya sulale da Yahaya Bello daga gidansa.

Gwamnan ya shiga har cikin gidan Yahaya Bello da aka kewaye inda ya fito da shi a sirrance a cikin motarsa ya wuce ta gaban jami'an EFCC

Lamarin ya faru ne yayin da hukumar EFCC ta yi wa gidan Yahaya Bello kawanya a birnin Abuja kan zargin badakalar N80bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.