Ana Cikin Nemansa, Yahaya Bello Ya Kalubalanci Hukumar EFCC
- Hukumar EFCC ba ta taɓa gayyatar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello domin ta yi masa tambayoyi a ofishinta ba
- Wannan ita ce matsayar ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello wanda a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, ya ce tsohon gwamnan ba ya tsoron hukumar
- Ofishin ya kuma ƙalubalanci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan da ta nuna alama a ɓainar jama’a cewa ta aike da takardar gayyata ga Yahaya Bello
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello ya yi iƙirarin cewa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ba ta taɓa gayyatar tsohon gwamnan na jihar Kogi ba.
Shugaban ofishin yaɗa labaran Yahaya Bello, Ohiare Michael, a wata sanarwa a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, shi ne ya bayyana hakan.
Ohiare Michael ya ce EFCC ba ta taɓa aika wa Yahaya Bello wani goron gayyata ba amma ta ci gaba da bayyana cewa ana nemansa, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ashe Yahaya Bello bai gujewa doka
Haka kuma da yake nanata cewa tsohon gwamnan ba mai gujewa doka ba ne, Michael ya buƙaci hukumar ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa ta gayyaci Bello domin yi masa tambayoyi, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.
"Ya kamata kowa ya sani cewa Alhaji Yahaya Bello ba ya tsoron EFCC, ba mai laifi ba ne wanda ya gujewa doka. Abin da ya ke bukata shi ne a mutunta doka."
“Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta gayyaci Alhaji Yahaya Bello bayan wa’adinsa ya ƙare a ranar 27 ga watan Janairun 2024. Muna ƙalubalantar EFCC da ta buga kwafin gayyatar da aka kai wa Yahaya Bello."
"Hakazalika su gaya wa ƴan Najeriya ranar da aka kai gayyatan da wanda aka kai wa. Muna da tabbacin hukumar EFCC ba za ta iya gabatar da ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ba, har zuwa yau ba su gayyaci Alhaji Yahaya Bello ba."
- Ohiare Michael
Yahaya Bello na tsoron kamu?
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a shirye yake ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan tuhume-tuhume 19 da ake zarginsa.
Sai dai tsohon gwamnan ta hannun lauyansa Lauyya bayyana yana da niyyar bayyana a gaban kotu, amma yana tsoron hukumar EFCC ta cafke shi kuma ta tsare shi a hannun ta.
Asali: Legit.ng