Dangin Amarya Sun Nuna Jarumta, Sun Afkawa Ƴan Bindiga Yayin da Suka Tare Su a Zamfara
- Dangin amarya da fasinjoji sun nuna jarumta yayin da suka afkawa ƴan bindigar da suka tare su a titin Talatan Mafara zuwa Gusau
- Rahoto ya nuna cewa sun yi nasarar daƙile yunƙurin ƴan bindigar na sace amarya kuma sun kashe ɗaya daga cikin ƴan ta'addan
- Amma ɗaya daga cikin fasinjojin ya rasu sakamakon bugawar zuciya bayan ganin abin da ya faru a gabansa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - A wata jarumta da ba kasafai ake samun irinta ba, dangin wata amarya da ake daf da ɗaura mata aure sun daƙile harin garkuwa da mutane a Zamfara.
A cewar PRNigeria, lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan bindiga suka yi wa dangin amaryar da wasu matafiya kwanton bauna a titin Talata Mafara zuwa Gusau.
An tattaro cewa dangin amaryar sun kama hanyar zuwa Kano ne domin siyo kayayyakin aure da tufafi amma ba zato ba tsammanin ƴan bindigar suka tare su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau ya bayyana cewa ƴan uwan amaryar da sauran fasinjojin motar sun yi kukan kura sun ɗauki mataki ne yayin da ƴan bindiga suka yi yunkurin sace su.
Yadda fasinjoji suka gwabza da 'yan bindiga
Duk da ɗaya daga cikin ƴan bindigar ya gudu, amma jajirtattun fasinjojin sun kwato bindigun AK47 guda biyu na maharan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Da yake ba da labarin yadda lamarin ya faru, ganau ya ce:
"Saura kiris su isa shingen binciken Fangal Tama kwatsam matafiyan suka fara jiyo ƙarar harbe-harbe, bisa mamaki sai suka ga ƴan bundiga biyu sun toshe titin.
"Nan take suka umarci budurwar (amaryar da ke dab da shiga daga ciki), mahaifi da mahaifiyarta da ƴan uwanta biyu su fito daga motar, suka tilasta musu shiga cikin daji.
"Da suka fahimci haɗarin da suka shiga, nan take fasinjojin suka yi kukan kura suka afkawa ɗaya daga cikin ƴan bindigar, suka danne shi har ya mutu, ɗayan kuma ya tsere ya bar bindigarsa.
Ina aka kai makaman 'yan bindiga?
Mutumin ya kara da cewa dangin amaryar da fasinjojin sun miƙa makaman ga dakarun sojoji da ke shingen bincike mafi kusa bayan sun samu nasara.
Amma duk da jarumtar da tawagar matafiyan suka nuna, ɗaya daga cikinsu zuciyarsa ta buga saboda abin da ya gani kuma an tabbatar da rai ya yi halinsa a asibiti.
Aliyu Usamatu, wani mazaunin yankin ya shaidawa Legit Hausa cewa wanda ya mutu kawun abokinsa ne kuma tuni aka masa jana'iza.
Ya ce:
"Wannan gaskiya ne kuma a zahirin gaskiya kowa ya ji daɗin abin da ya faru, wanda ya mutu kawun abokina ne, Allah ya jiƙansa ya masa rahama ya kawo mana ƙarshen wannan matsala."
Soja ya kashe farar hula
A wani rahoton kuma wani soja da ke murnar zagayowar ranar haihuwarsa ya bindige wani mutumi har lahira a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato.
Ƙungiyar BCDC ta yi tir da lamarin kuma ta nuna rashin jin daɗinta kan yadda sojoji ke yunkurin lakabawa waɗanda ba ruwansu.
Asali: Legit.ng