Gwamnatin Najeriya Ta Ci Gaba da Gurfanar da Ƴan Ta'addan da Ta Kama a Gaban Kotu
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tuni ta ci gaba da gurfanar da ƴan Boko Haram da ta kama a gaban ƙuliya domin a hukunta su
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribaɗu ne ya tabbatar da haka a wurin taron yaƙi da ta'addanci a Abuja
- NSA ya ce Najeriya ta ɓullo da sabbin hanyoyin yaƙi da ta'addanci ciki har da amfani da fasahar zamani domin kawo ƙarshen lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ci gaba da shari'a kan ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram da ke tsare a Kainji.
Mai bai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu ne ya bayyana haka a wajen taron yaki da ta'addanci na kasashen Afrika na kwanaki biyu a Abuja.
Ta'adin Boko Haram da 'yan ta'addan ISWAP
A cewarsa, Najeriya tana kuma tattara bayanan sirri kan ayyukan kungiyar Boko Haram da kungiyar ISWAP domin kakkaɓe ta'addancisu a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Ribadu ya ce taron ya ƙara nuna dabaru da shirin Najeriya wajen aiwatar yarjejeniyar yaki da ta’addanci ta majalisar dinkin duniya.
Afirka na fama da ƙalubalen tsaro
NSA ya ƙara da cewa nahiyar Afirka na fuskantar barazana daga kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban waɗanda ke addabar mutane marasa ƙarfi.
Ya ce Gwamnatin Najeriya ta ƙara fadada hanyoyin da za ta bi wajen tunkarar matsalar tsaro musamman waɗanda suka samo asali daga ayyukan Boko Haram da ISWAP.
Daga cikin hanyoyin da Najeriya za ta yi amfani da su wajen kawar da ayyukan ta'addanci har da amfani da fasahohin zamani, in ji Malam Nuhu Ribaɗu.
A nasa bangaren, mataimakin babban sakataren UN mai kula da yaki da ta'addanci, Vladimir Voronkov, ya ce majalisar ta samu nasara ne bisa goyon bayan ƙasashen Afrika.
A cewarsa, nasarorin da majalisar ɗinkin duniya (UN) ta samu suna da alaƙa da haɗin guiwar ƙasashen Afirka wajen lalubo mafita, jaridar Guardian ta ruwaito.
Tinubu ya halarci taron tsaro
Ana sa ran babban taron na kwanaki 2 zai lalubo mafita ga matsalolin tsaro da dama da suka addabi Najeriya da Afirka baki daya.
Taron dai ya samu halartar shugaba Bola Tinubu, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, da shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe.
Shugaba Jonathan ya faɗi mafita
Rahoto ya zo cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a ƙasar nan.
Jonathan ya bayyana cewa ba za a samu ingantaccen tsaro a ƙasar nan ba har sai an samar da ƴan sandan jihohi.
Asali: Legit.ng