Sanata Marafa Ya Caccaki Ministan Shugaba Tinubu Kan Sukar Dattawan Arewa

Sanata Marafa Ya Caccaki Ministan Shugaba Tinubu Kan Sukar Dattawan Arewa

  • Tsohon Sanatan Zamfara ta tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana cewa dattawan Arewa ba nauyi ba ne da ya damu ƴan Arewa
  • Marafa a cikin wata sanarwa ya ce cin mutuncin dattawan Arewa tamkar cin mutuncin al’ummar yankin ne baki ɗaya
  • Tsohon sanatan wanda da shi aka kafa jam'iyyar APC ya ce ya kamata Matawalle ya nemi afuwa a wajen dattawa da ƴan Arewa baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Tinubu/Shettima 2023 a jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya caccaki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Kabiru Marafa ya caccaki tsohon gwamnan na jihar Zamfara ne kan kiran Dattawan Arewa a matsayin wani nauyi da ya damu ƴan Arewa.

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin addinin da 'yan bindiga suka sace ya shaki iskar 'yanci

Marafa ya caccaki Matawalle
Marafa ya caccaki Matawalle kan sukar Dattawan Arewa Hoto: @AAAdeyeye, @Bellomatawalle1
Asali: UGC

Marafa ya yi kira ga Matawalle da ya janye kalaman nasa, ya kuma nemi afuwa daga wajen dattawan Arewa da ƴan Arewa baki ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Me Marafa ya ce kan kalaman Matawalle?

'Dan siyasar ya ce cin mutuncin da ministan ya yi na Dattawan Arewa tamkar cin mutuncin al’ummar yankin ne baki ɗaya.

Ya buƙaci yankin Arewa da ya yi watsi da kalaman na tsohon gwamnan jihar Zamfara domin ya san cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu yana girmama Arewa, ƴan Arewa, da shugabanninsu, inji rahoton The Punch.

"Ina so in bayyana cewa wannan ra'ayi da Matawalle ya bayyana ra'ayinsa ne na kansa ba na shugaban ƙasa ko fadar shugaban ƙasa ba, don haka ya kamata a yi watsi da shi."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe bayin Allah sama da 20 a Kaduna

"Na san tabbas Arewa, ƴan Arewa da Dattawan Arewa ba nauyi ba ne wajen gudanar da abubuwa a yankin da ƙasa baki ɗaya. Shugaban ƙasa yana da wannan ra'ayi, saboda haka yana tare da ni a kan wannan."

- Kabiru Marafa

Matawalle ya ƙalubalanci ƴan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya ƙalubalanci dukkan waɗanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa mukami a Arewa.

Matawalle ya ce ya kamata dukkansu su fito su kare shugaban ƙasan yayin da ya ke fuskantar kushewa da suka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng