UTME 2024: Hanyoyin da Dalibai Za Su Bi Cikin Sauki Su Ci Maki Mai Yawa a Jarrabawar JAMB
- An shawarci daliban da ke shirin rubuta jarrabawar UTME ta JAMB a bana kan yadda za su samu nasarar cin jarrabawar cikin sauki
- Osunwoye Samuel, wani mai hidimar daura ‘yan JAMB a turban a tsawon lokaci ya tattauna da Legit kan yadda dalibai za su shawo kan lamarin UTME
- A cewar masanin, ana sa ran daliban da za su rubuta UTME a bana su kasance masu daidaitaccen ilimi na na’ura mai kwakwalwa gabanin jarrabawar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - An shawarci dukkan daliban da ke shirin rubuta jarrabawar UTME a bana da su kasance masu zaman shiri da sanin wasu abubuwa masu muhimmanci.
A ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu ne hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba sakandare JAMB ta fara gudanar jarrabawar UTME na 2024.
A tattaunawar da Legit ta yi da Osunwoye Samuel, wani masani kuma mai taimakawa dalibai su tsallake jarrabawar UTME, ya fadi abubuwan da daliban ya kamata su maida hankali a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hanyar da dalibai za su bi su ci JAMB
Da yake bayani ga wakilinmu, ya ce:
“Dole ne dalibai su yi karatu tukuru kuma su kasance masu wayo wajen gane ingantattun amsoshi a cikin dan gajeren lokaci. Wato, kada dalibai su bata lokaci haka siddan kan tambayoyin da basu cancanta ba saboda tambayoyi na iya daukar maki daya amma ba sa daukar matsayi daya.
“Dole ne dalibai su kasance suna da ilimin tushe game da amfani da kwamfuta; tarihi ya bayyana yadda wasu daliban UTME da ba su iya kwamfuta suka fadi jarrabawarsu saboda rashin kwarewa ko tsoron amfani da kwamfuta.
“Daliban da ke da wannan matsalar da ba su da kwamfuta za su iya sauke daya daga manhajar JAMB CBT Practice Offline-APP ko dai wata manhaja a Play Store ko Google Store, ko kuma kawai za su iya nemowa kai tsaye a Google don gwada jarrabawar JAMB ta CBT. Da wannan, za su iya yin jarrabawar gwaji iya adadin da suke so.
"Idan dalibi ya gamu da wata tambaya mai wahala, zan ba da shawarar cewa ya tsallake ta ta hanyar danna "NEXT" akan allon bugu.
“Wannan zai baiwa dalibin damar gwada dukkan tambayoyin da kuma adana lokaci. Bata lokaci mai yawa a tambayar da ke da wuya wanda a karshe zaku iya kuskuren amsawa zai bata lokaci ne kawai, kuma zai hana dalibai damar amsatambayoyin masu sauki a gaba.”
Za a kama iyayen da ke shawagi a kusa da cibiyoyin jarrabawar UTME
A wani labarin, kun ji yadda aka gargadi iyaye kan cewa, su guji shawagi a kusa da inda ake rubuta jarrabawar UTME a 2024.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da za a fara jarrabawar a Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Jarrabawar JAMB ce hanyar da dalibai a Najeriya ke samun damar shiga jami'a don yin karatun digiri.
Asali: Legit.ng