"Ɗaurin Shekaru 5": EFCC Ta Ja Kunnen Gwamna da Masu Kawo Cikas Kan Yahaya Bello

"Ɗaurin Shekaru 5": EFCC Ta Ja Kunnen Gwamna da Masu Kawo Cikas Kan Yahaya Bello

  • Hukumar EFCC ta gargaɗi duk wani mai kokarin daƙile yunkurin jami'anta yayin gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada
  • Wannan gargaɗi da jan kunne na zuwa ne yayin da Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya daƙile yunkurin cafke Yahaya Bello a Abuja
  • Tun farko, jami'an hukumar EFCC sun kewaye gidan Yahaya Bello kuma sun fara shirin kama shi da karfi kafin zuwan gwamnan Kogi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) ta yi gargadin cewa ba za ta sake lamuntar wani ya kawo mata cikas a ayyukanta ba.

EFCC ta yi wannan gargaɗi ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter da daren ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Wawure N80bn: EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamna da wasu mutum 3 a gaban kotu

Gwamna Yahaya Bello da EFCC.
EFCC ta gargaɗi masu kawo mata cikas a ayyukanta a Najeriya Hoto: Alhaji Yahaya Bello, EFCC
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar ta yi rashin nasara a yunkurinta na cafke tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ranar Laraba a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Yahaya Bello ya tsira daga EFCC

An ce a lokacin da gwamnan jihar Kogi mai ci, Usman Ododo, ya isa gidan magabacin nasa, jami’an tsaro na shirin kama Bello da karfin tsiya.

Legit Hausa ta tattaro muku yadda jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa suka kai samame gidan Yahaya Bello a Wuse Zone 4, Abuja.

Bayan jiran sa'o'i, EFCC ta ƙara girke ƙarin jami'anta a layin Benghazi a wani yunƙuri na kama tsohon gwamnan da ƙarfi kamar yadda ta yi wa tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha.

Ana cikin haka ne Gwamna Usman Ododo ya isa gidan kuma ba tare da jimawa ba ya fito ya bar wurin, inda rahotanni suka nuna Yahaya Bello na cikin motarsa.

Kara karanta wannan

"Lamarin ya yi muni" Ƴan bindiga sun kewaye gari guda, sun tafka mummunar ɓarna a Kaduna

Hukumar EFCC ta aika da gargaɗi

Da yake mayar da martani kan wannan dambarwa, kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya yi gargaɗin cewa babban laifi ne daƙile jami'an hukumar daga gudanar da aikinsu.

Sanarwar ta ce:

"Sashe na 38 (2) (a (b) na dokar kafa hukumar EFCC, ya tanadi cewa hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na doka babban laifi ne kuma duk wanda ya yi hakan za a ɗaure shi na abin da bai gaza shekaru biyar ba a gidan yari."

Kakakin na EFCC ya bayyana cewa daga yanzu ba za su sake lamuntar wani mutum ko kungiya su kawo masu cikas a ayyukansu ba, za su ɗauki matakin da ya dace.

Kotu ta hana EFCC kama Yahaya Bello

A wani rahoton na daban Kotu ta hana hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta kama, tsare da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello

Alƙalin kotun watau mai shari'a I. A Jamil ya tabbatar wa da tsohon gwamnan haƙƙinsa na zama ɗan adam, ya ce bai halatta a tauye masa haƙƙi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262