Jimami Yayin da Tsohon Sanata Ibrahim Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Bayanai Sun Fito

Jimami Yayin da Tsohon Sanata Ibrahim Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Bayanai Sun Fito

  • Tsohon sanatan jihar Kwara, Rafiu Ibrahim, ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 57 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Iyalan marigayin ne suka bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, sun ce za a masa jana'iza nan ba da jimawa ba
  • Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi ta'aziyyar rasuwar Sanata Rafiu Ibrahim, inda ya ce labarin ya girgiza shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Sanata Rafi'u Adebayo Ibrahim, tsohon sanata daga jihar Kwara da ke Arewa da Tsakiya, ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon mamban majalisar dattawan ya rasu ne yana da shekaru 57 a duniya bayan fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar tsohon dan Majalisar Tarayya a Kwara, Sanata ya tafka babban rashi

Sanata Rafiu Ibrahim.
Tsohon sanatan Kwara ya kwanta dama da shekaru 57 Hoto: Senator Rafiu Ibrahim
Asali: Twitter

Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwar Sanata Ibrahim a wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, sanarwan ta ce za a yi wa marigayin sallar Jana'iza nan ba da jimawa ba.

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Muna rokon Allah SWT ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makoma a gare shi, Ameen."

Gwamna AbdulRazaq ya yi ta'aziyya

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya aike da saƙon ta'aziyya bisa rasuwar tsohon sanatan.

Gwamnan ya ce ya kaɗu da jin labarin rasuwar Sanata Ibrahim na jam’iyyar PDP sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

AbdulRazaq ya ce:

"Wannan abu ne mai matuƙar tada hankali da ke tunatar damu cewa mutuwa tana wuyan kowane ɗan adam kuma ita mutuwa tana zuwa ne ba tare da sanarwa ba.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa" Gwamna Sule ya jero ƙananan hukumomi 8 da ke cikin babbar matsala

Da yake ta'aziyyar rasuwar sanatan, Barista Titilope Anifowoshe, kwararren lauya kuma fitaccen dan jihar Kwara, ya bayyana rasuwar tsohon dan majalisar a matsayin abu mai taɓa zuciya.

Anifowoshe, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar Laraba, ya bayyana cewa Sanata Ibrahim ya yi fice wajen kyautatawa, ba wai ga ‘yan jam’iyyarsa kadai ba.

Sanatan Kwara ya rasa mahaifi

A wani rahoton kuma kun ji cewa Mahaifin sanatan da ke wakiltar Kwara ta Arewa , Sadiq Umar ya riga mu gidan gaskiya a jihar.

Marigayin mai suna Alhaji Suleiman Omar ya rasu ne a daren jiya Talata 16 ga watan Afrilu a jihar Kwara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262