An Damke Mutane Sun Yi Karyar an Yi Garkuwa da Su, Sun Bukaci Fansar Miliyoyin Kudi
- Wasu mutane uku sun shirya makircin garkuwa da kansu kuma sun bukaci a biya su miliyoyin kudi daga kamfanin da suke aiki a jihar Edo
- Kakakin rundunar'yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma nasarar cafke su
- Har ila yau, kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana dabarun da suka yi wajen gano makircin da mutanen suka kulla
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Rundunar ‘yan sanda a jihar Edo ta kama wasu mutane uku bisa zarginsu da laifin shirya garkuwa da kansu da kuma neman kudin fansa.
Mutanen wadanda suka hada da Blessing Ogunu, Esther Anthony da Ukpebor Joel sun kuma neman a biya su N4,800,000 kudin fansa daga kamfaninsu.
Yadda rahoton yazo wa 'yan sanda
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya bayyana cewa wani mai suna Samuel Prince Omomuzo ya kai wa ‘yan sanda rahoton cewa an yi garkuwa da Blessing, ma’aikaciyar Bliss Legacy Limited da ke garin Benin da wasu mata biyu Esther da Joel a Benin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jaridar Daily Trust mutumin ya kara cewa masu garkuwa da mutane sun bukaci N4.8m daga kamfanin.
Ta ya jami'an tsaro suka gano su
Kakakin 'yan sandan yace sun gano su ne ta hanyar amfani da bayanan fasaha, cewar jaridar PM News.
Ya ci gaba da cewa a yayin da ake yi masu tambayoyi, Blessing ta amsa cewa ta shirya garkuwar ne saboda kamfaninta ya ki bai wa wani abokin cinikinsu fili da suka riga suka karbi kudi a wajensa.
Ma'aurata sun yi karyar garkuwa da su
Haka zalika kun ji cewa 'yan sanda sun kama mata da miji da suka yi karyar an yi garkuwa da su don su samu kudin fansa har naira miliyan biyar
Hankulan iyalan ma'auratan ya tashi bayan da aka kira su a waya aka nemi kudin fansar, inda suka shigar da karar lamarin ga 'yan sanda
Sai dai bayan tsananta bincike, jami'an tsaron sun gano ma'auratan, wadanda kuma suka amsa laifin su tare da fadin dalilin yin karyar
Asali: Legit.ng