'Yan Bindiga Sun Yi Sabuwar Ta'asa Ta Kashe Mutane a Jihar Kaduna

'Yan Bindiga Sun Yi Sabuwar Ta'asa Ta Kashe Mutane a Jihar Kaduna

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun sake kai harin ta'addanci a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
  • Mutum uku sun rasa rayukansu a yayin harin sannan tsagerun sun kuma yi awon gaba da wasu mutum bakwai zuwa cikin daji
  • Ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin duk da bai yi cikakken bayani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum uku a wani hari da suka kai wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa ƴan bindigan sun kai harin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024.

Kara karanta wannan

"Lamarin ya yi muni" Ƴan bindiga sun kewaye gari guda, sun tafka mummunar ɓarna a Kaduna

'Yan bindiga sun hallaka mutum uku a Kaduna
'Yan bindiga sun kai sabon hari a kauyukan jihar Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindiga suka kai harin

Mazauna yankin sun bayyana cewa an hallaka mutum biyu a wani ƙauye da ke kusa da Anguwar Tanko Dogon Sarki da ke ƙarƙashin mazaɓar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari da misalin ƙarfe 9:00 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun kuma kai hari ƙauyen Rafin Gora mai tazarar kilomita biyu daga yankin Dogon Dawa da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar, inda suka kashe wani mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai.

'Yan bindiga sun dauke mutane a Kaduna

Wani mamban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya tabbatar da faruwar harin na Anguwar Tanko Dogon Sarki, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya kuma ƙara da cewa a wannan rana ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane a ƙauyen Tashar Kaji da ke ƙarƙashin mazaɓar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutum 45 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar sabuwar cuta

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar harin na ƙauyen Rafin Gora sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan sauran abubuwan da suka faru ba.

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansur Hassan, saboda bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

Ƴan bindiga sun hallaka ɗan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kashe wani jami’in ɗan sanda a wani hari da suka kai kan shingen bincike a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Tsagerun ƴan bindigan sun kuma ƙona motar da ƴan sandan suke aikin sintiri da ita bayan sun farmake su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng