Binciken El-Rufai: An Bayyana Dalilin Kafa Kwamitin Bin Diddikin Ayyukan Tsohon Gwamnan

Binciken El-Rufai: An Bayyana Dalilin Kafa Kwamitin Bin Diddikin Ayyukan Tsohon Gwamnan

  • Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya yi magana kan dalilin da ya sa aka kafa kwamitin binciken Nasir El-Rufai
  • Liman ya bayyana cewa za a gudanar da binciken ne domin nuna cewa majalisar da yake jagoranta ba ta amshin shata ba ce
  • Ya yi nuni da cewa ba su yi yunƙurin gudanar da wannan binciken ba domin aibanta wani, inda ya bada tabbacin cewa za a yi adalci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya bayyana dalilin da ya sa majalisar ke binciken bashin da gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar, Malam Nasir El-Rufai ta karɓo.

Liman ya faɗi dalilin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilu, bayan da majalisar ta kafa wani kwamiti mai mutum 13 da zai yi bincike kan El-Rufai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dawo biyan tallafin man fetur, an bayyana kudin da take kashewa

Dalilin bincikar El-Rufai
An kafa kwamitin binciken Nasir El-Rufai a Kaduna Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ce gwamitin dai zai binciki lamuni, tallafi, da sauran ayyukan da aka aiwatar daga shekarar 2015 zuwa 2023 a lokacin El-Rufai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafa kwamitin na zuwa ne bayan Gwamna Uba Sani, ya ce gwamnatinsa ta gaji bashin dala miliyan 587 da N85bn, da kuma bashin kwangiloli 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Meyasa za a binciki El-Rufai?

Ya bada tabbacin cewa za a duba lamarin yadda ya kamata, yana mai cewa za su ba kowa ƴancin faɗin gaskiya.

"Muna so ne kawai mu yi nazari kan yadda gwamnatin da ta shuɗe ta kashe kuɗinta ta yadda za mu yi alfahari da kanmu zuwa lokacin da muka bar majalisa cewa mun yi abin da ya dace."
"Ba mu son wani ya kira mu da ƴan amshin shata, ba mu yin wannan binciken domin aibanta wani, amma za mu yi abin da ya dace."

Kara karanta wannan

El-Rufai ya shiga sabuwar matsala yayin da majalisar Kaduna ta kafa kwamitin bincike

- Yusuf Liman

El-Rufai ya faɗi hanyar maguɗi

A wani labarin kuma,.kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana hanyar.da gwamnoni ke bi suna yin maguɗin zaɓe.

El-Rufai ya yi nuni da cewa gwamnoni na amfani da hukumomin zaɓe na jihohi domin yin maguɗin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng