Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Farmaki Hedkwatar Ƙaramar Hukuma, Sun Tafka Ɓarna
- Wasu mahara da ake zaton ƴan bindiga ne sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar Ilejemeje a jihar Ekiti ranar Talata
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun buɗe wuta yayin harin, lamarin da ya jefa ma'aikata cikin firgici da tashin hankali
- Shugaban ƙaramar hukuma, Hon. Alaba Dada, ya ce ana zargin maharan sun fito ne daga wani ƙauye da ke jihar Kwara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ekiti - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai ƙazamin farmaki a sakateriyar ƙaramar hukumar Ilejemeje da ke garin Eda-Oniyo a jihar Ekiti.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro, wannan lamarin ya haifar da firgici da tashin hankali a tsakanin ma'aikatan da ke sakateriyar ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.
Wannan kazamin hari na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan wasu ƴan fafutukar kafa kasar Yarbawa sun kutsa kai cikin gidan gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi ɓarna
Ƴan bindigar da suka kai harin Ekiti, waɗanda suka shiga sakateriyar ƙaramar hukumar ɗauke da makamai, sun saki wuta da bindigoginsu yayin harin.
Makaman da aka ga maharan ɗauke da su sun haɗa da bindigu, layu, wuƙaƙe da sauran miyagun makamai, rahoton Daily Post.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun lalata gine-gine da kadarori masu yawa da ake ajiye a cikin hedkwatar ƙaramar hukumar Ikejemeje a jihar Ekiti.
A yayin harin wanda ya dauki tsawon sa’o'i, mutum guda ya samu munanan raunuka, kuma an garzaya da shi asibitin kwararru na jihar da ke Iye-Ekiti domin samun kulawar gaggawa.
Shugaban karamar hukuma ya tabbatar da harin
Shugaban karamar hukumar Ilejemaje, Mista Alaba Dada, ya ce suna zargin ‘yan bindigar sun fito ne daga kauyen Obbo-Ayegunle ne a jihar Kwara.
Ya alaƙanta wannan hare-hare da taƙaddamar filaye da ke wakana tsakanin kauyukan biyu amma ya ƙara da cewa an tura ƙarin jami'an tsaro domin daƙile harin ɗaukar fansa.
Ya ce akwai bukatar gwamnatocin jihohin Ekiti da Kwara su haɗu su sasanta rikicin filaye domin samun zaman lafiya da zumunci a tsakanin al'umma.
Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP
A wani rahoton kuma Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin ISWAP da wasu mayaƙansu a jihar Borno.
Kakakin rundunar NAF, AVM Edward Gabwet ya ce wannan samamen ya lalata muhimman kayayyakin ƴan ta'addan a gabar tafkin Chadi.
Asali: Legit.ng