Mace Ko Namiji: Jami’in Gidan Yarin Kirikiri Ya Bayyana Yadda Suke Mu’amalantar Bobrisky

Mace Ko Namiji: Jami’in Gidan Yarin Kirikiri Ya Bayyana Yadda Suke Mu’amalantar Bobrisky

  • Al’amura na tafiya yadda ya kamata game da Idris Okuneye (wanda aka fi sani da Bobrisky) a gidan gyaran hali, a cewar wani ganduroba
  • Jami’in ya shaida wa manema labarai cewa, yayin da Bobrisky ke biyayya ga dokokin gidan yari, ana mu’amalantarsa kamar sauran fursunoni
  • Har ila yau, an bayyana cewa, babu wata matsala ta daidaitar jinsi tattare da mai kamceceniya da shigar matar, Bobrisky

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas – An bayyana yadda Idris Okuneye (wanda aka fi sani da Bobrisky) ke fama da yanayi a gidan yarin Kirikiri da ke jihar Legas.

Gidan yarin Kirikiri ya magantu kan rayuwar Bobrisky tare da fursunoni
Jami’in gidan yarin Kirikiri ya bayyana yadda cewa Bobrisky ba mata maza bane. Hoto: bobrisky222
Asali: Instagram

Kirikiri: Yadda ake mu'amalantar Bobrisky

Wani babban ganduroba da ya yi magana da ‘yan jarida kan halin Bobrisky a gidan yari ya ce yana kiyaye duk ka’idojin gidan yarin kamar yadda ake sa rai.

Kara karanta wannan

"Ina cikin mawuyacin hali": Adam A Zango ya koka kan rashin samun farin ciki a rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar SaharaReporters ta rahoto jami’in ya kara da cewa tun lokacin da wanda aka yanke wa hukuncin ya shiga gidan yarin ake mu’amalantarsa kamar sauran fursunoni.

Jami'in ya ce:

"... an ware masa wani daki, kuma an hada shi da wasu adadin fursunoni. An ba shi gadon kwanciya shi kadai. “Idan lokacin aji ya yi yana shiga, idan lokacin cin abinci ya yi, zai je ya karbo nasa.
"Tun da aka shigo da shi nan yake gudanar da harkokinsa kamar sauran fursunoni, kama daga lokacin amsa kiran sunaye ko idan za a kwanta bacci"

Jami'in gidan yari kan jinsin Bobrisky

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa daga bincike da kuma lura da wanda aka yankewa laifin an gano shi ba mata-maza bane a bangaren jinsi, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

Ya bayyana cewa:

"Bobrisky ya bayyana a fili cewa shi namiji ne kuma shari'ar kotu bayanan jama'a ne. Ana duba duk wani fursuna da aka shigo da shi gidan yarin, kamar yadda shi ma aka duba shi.
"Bayan an duba shi, an gano shi ba mata-maza bane a bangaren jinsi, duk wasu halittunsa na namiji suna nan a jikinsa ba tare da ragi ko kari ba."

Gemu ya fara fitowa Bobrisky

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa an gano gemu ya fara fitowa a habar fitaccen dan daudun nan Okuneye Idris Olanrewaju, da aka fi sani da Bobrisky.

A halin yanzu dai Bobrisky na zaune a gidan yarin Kirikiri bayan da kotun Legas ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida ba tare da biyan tara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.