Tashar Wutar Lantarkin Kasar Nan Ta Dauke a Karo na 6 a Shekarar Bana

Tashar Wutar Lantarkin Kasar Nan Ta Dauke a Karo na 6 a Shekarar Bana

  • A karo na shida, tashar wutar lantarki ta kasa ta lalace tun safiyar yau Litinin wanda hakan ya jefa jama'a cikin duhu
  • Wannan na nufin za a samu raguwar rarrabuwar hasksen wutar lantarki ga kwastotmomin kamfanonin duk da karancinta da 'yan kasa ke fuskanta
  • Shugaban kamafanin rarraba hasken wutar lantarki a Jos ya ce suna fatan za a gyara wutar nan kusa domin ba su damar rarraba ta ga kwastotmominsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Najeriya - Tashar samar da wutar lantarki ta Najeriya ta sake lalacewa karo na shida a cikin shekarar 2024, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Farashin kayayyaki ya fara sauka yayin da Naira ke ci gaba da yin daraja

Tashar ta samu matsala ne da misalin karfe 2.42 na safiyar yau, inda yanzu wutar da ake bayarwa ta fado zuwa megawatt 64.70 rak, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A bayanan da ISO dake samar da bayanai kan wutar lantarkin ya bayyana cewa kamfanin samar da wutar lantarki daya ne kacal, na Ibom Power ke aiki a yanzu.

Tashar wutar lantarki ta kasa
Wannan shi ne karo na 6 da Tashar ta lalace a shekarar nan Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tabbatar da lalacewar tashar, kamfanin samar da wutar lantarki a Jos ya ce:

“Rashin wuta da ake samu a jihohin da muke ba wuta ya samo asali ne saboda rashin wautar daga tashar samar da wuta ta kasa.
An samu katsewar samar da hasken wutar lantarkin a safiyar yau da misalain karfe 2.42, 15 ga watan Afrilu 2024, wanda ya haddasa rashin wuta ga dukkanin wuraren ajiyar wutar.”

Kara karanta wannan

Ma’aikatan lantarki sun juyawa gwamnati baya, sun bukaci a janye karin kudin wuta

Shugaban kamfanin, Dr. Friday Adakole Elijah ya bayyana fatan dawowar wutar domin su ci gaba da rarraba ta ga abokan hulda.

TCN na kokarin gyara tashoshin rarraba wuta

Lalacewar tashar lantarkin a yau na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na kasa (TCN) ke kokarin gyara wasu tashoshin.

Vanguard News ta ruwaito cewa TCN na fafutukar gyara tashoshin yayin da kamfanonin rarraba hasken wutar da ke Abuja, Ibadan, Legas da Benin.

An samu daukewar wuta a wasu jihohi

Rahotannin da Legit Hausa ta samu ya tabbatar da cewa an samu matsalar daukewar hasken wutar lantarki a wasu jihohin dake Arewacin kasar nan.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da Kaduna, Sokoto, Zamfara, da jihar Kebbi bayan kamfanin rarraba wutar dake Kaduna ya rasa kaso mai tsoka na hasken wutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.