FIRS Ta Fadi Adadin Tiriliyoyin da Gwamnatin Najeriya Ta Samu Daga Haraji a 2023
- Hukumar FIRS ta bayyana cewa abin da ta samu daga haraji a shekarar da ta gabata ya zarce Naira Tiriliyan 12.3
- Zacch Adedeji wanda shi ne shugaban FIRS ya bayyana wannan lokacin da ya ziyarci kasuwar duniya da ke ci a Enugu
- Wata babbar jami’ar hukumar ta wakilci Zacch Adedeji, ta yi bayanin nasarorin da aka samu ta fuskar haraji a 2023
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Enugu - Shugaban hukumar FIRS mai alhakin tattara haraji a Najeriya, Zacch Adedeji ya ce sun samu gagarumar nasara a bara.
Mr Zacch Adedeji ya ce a shekarar 2023 da ta gabata, FIRS ta samu Naira tiriliyan 12.3.
Aisha Ribadu ta wakilci shugaban FIRS
Wata babbar jami’ar hukumar ta FIRS, Aisha Ribadu ta wakilci shugaban nata a wajen bikin bude taron kasuwar duniya a Enugu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Guardian ta ce kungiyar ECCIMA ta ‘yan kasuwa da manoma ta reshen jihar Enugu ta gayyaci shugaban FIRS zuwa baja-kolin.
Sirrin nasarar shugaban hukumar FIRS
A jawabin Mrs Aisha Ribadu, ta bayyana cewa an samu wadannan nasarori ne saboda jajircewa da yadda aka karfafa ma’aikata.
Zacch Adedeji ya godewa ECCIMA da ta ba shi damar yin jawabi a wajen wannan taro da aka zabawa take na musamman a bana.
Idan aka maida hankali wajen kawo cigaban al’umma, shugaban na FIRS ya ce za a samu cigaba mai dorewa yayin da ake kukan kudi.
Jawabin na Adedeji ya kunshi bayanin sauye-sauye da aka samu a hukumar FIRS domin ganin an fadada hanyar samun kudin shiga.
Daga ciki shi ne fito da wata fasahar zamani domin ma’aikatan haraji su yi iya aikin karbar haraji a ko ina kuma a kowane lokaci a kasar.
ECCIMA ta ba Hukumar FIRS shawara
The Nation ta ce shugaban ECCIMA, Odeiga Jideonwo ya gabatar da jawabin bude taro.
Odeiga Jideonwo ya samu wakiltar Nnanyereugo Onyemelukwe wanda ya ba FIRS shawarar yadda za ta inganta aikin haraji.
Ana zargin Ganduje da cin kudi
A babin siyasa, ana da labari cewa da aka ba NNPP gaskiya a shari’ar zaben Kano, sai aka fara zancen Abba Yusuf zai dawo APC.
A yau kuwa gwamna Abba ya hurowa Dr. Abdullahi Umar Ganduje wuta cewa sai an bincike shi saboda taba dukiyar jihar Kano.
Asali: Legit.ng