Sanata Yari Ya Kawo Mafita Ga Ƴan Najeriya Kan Ƙoƙarin Tinubu Na Kawar da Ƴan Bindiga
- Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya buƙaci ƴan Najeriya su dage da yi wa Bola Tinubu addu'a a kokarinsa na tabbatar da tsaro a ƙasar nan
- Sanata Abdul'aziz Yari ya ce duk wasu matakai da ya kamata, tuni gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauka saura kawai addu'a
- Ya kuma bayyana shirinsa na faɗaɗa tallafin da yake rabawa mutanen mahaifarsa zuwa fannin ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sanata Abdul'aziz Yari ya yi kira ga ƴan Najeriya su dage da yi wa Gwamnatin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, addu'a domin ta yi nasara a yaƙin da take da matsalar tsaro.
Yari ya yi wannan kiran ne a wurin ganawarsa da kwamitin da ya dorawa alhakin rabon tallafin watan Ramadan ga magidanta 250,000 a mahaifarsa Talata Mafara da ke jihar Zamfara.
Sanata Yari, tsohon gwamnan jihar Zanfara ya ce a yanzu yi wa Tinubu addu'a ya zama tilas domin ya mayar da hankali da hikima har Allah ya ba shi nasara, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shugaban Ƙasa Tinubu ne babban kwamandan dakarun sojojin Najeriya kuma duk wasu matakai da ya kamata a ɗauka gwamnatin Tinubu ta ɗauka domin dawo da tsaro.
"Saboda haka yanzu zabi ɗaya tilo da ya rage shi ne addu'a domin a samu nasara a wannan yaƙi."
- Abdul'aziz Yari.
Yari zai bada tallafin karatu
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa yana shirin kara yawan wadanda za su amfana da wannan tallafin zuwa magidanta tsakanin 500,000 zuwa 700,000.
Sanata Yari ya kuma yi alƙawarin faɗaɗa shirin tallafawa mutane zuwa ɓangaren ilimi, inda ya ce zai zaƙulo maɓukata a fannin domin agaza masu su nemi ilimi.
Ya bai wa kwamitin umarnin su tantance dukkan ƙananan yaran waɗannan magidanta masu ƙaramin karfi domin su ci moriyar tallafi da zai bayar na karatu.
Sanatan ya nuna farin cikinsa bisa yadda kwamitin ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da rikon amana yayin rabon kayan tallafin a watan Ramadana, cewar Tribune Nigeria.
Matawalle ya caccaki NEF
A wani rahoton kuma Matawalle ya caccaki ƙungiyar dattawan Arewa NEF kan kalaman sukar da ta yi wa gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
Ƙaramin ministan tsaron ya ce kungiyar ba ta iya tsinanawa Arewa komai, ta zama tamkar nauyi ga ƴan Arewa
Asali: Legit.ng