Bola Tinubu Ya Faɗi Watan da Ƴan Najeriya Za Su Fita Daga Ƙangin Tsadar Rayuwa a 2024

Bola Tinubu Ya Faɗi Watan da Ƴan Najeriya Za Su Fita Daga Ƙangin Tsadar Rayuwa a 2024

  • Duk da ana fama da yunwa da hauhawar farashin kayayyaki, Bola Ahmed Tinubu ya roki ƴan Najeriya su haɗa kai kuma kada su karaya
  • Shugaban ƙasar ya faɗa wa ƴan Najeriya cewa su kwana da shirin cewa tattalin arziki zai farfaɗo daga nan zuwa watan Disamba, 2024
  • Tinubu ya kuma roƙi gwamnoni su haɗa kai kuma su tabbata Najeriya ta c< gaba, yana mai cewa aiki tare shi ne mabuɗin nasara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Duk da wahalhalu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa tattalin arzikin kasar "zai daukaka" nan da Disamba 2024.

Tinubu ya kuma yi kira da a hada kai kan manufa ɗaya tare da zurfafa hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kuma ‘yan majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

"Makaho ne kaɗai zai ce Tinubu ya gaza" Minista ya maida zazzafan martani ga NEF

Bola Ahmed Tinubu.
Yan Najeriya za su tsira daga yunwa da wahala a watan Disamba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me zai faru a watan Disamba?

Shugaban ƙasar ya ce haɗin guiwa tsakanin FG, gwamnoni da ƴan majalisar tarayya zai taimaka wajen cimma kowace irin manufa ƙasar nan ta sa a gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Tattalin arzikinmu ya yo kwana. A cikin ƴan watanni masu zuwa, tattalin arzikin zai koma layin daukaka. Zuwa Disamba, ina fata za mu samu dalilin da zamu yi murna."

- In ji Bola Tinubu lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnoni da ƴan majalisar tarayya waɗanda suka kai masa ziyarar barka da Sallah a Legas ranar Jumu'a.

Wannan tabbaci da Tinubu ya ba ƴan Najeriya na kunshe a wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar 12 ga watan Afrilu.

Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya wallafa sanarwar a shafinsa na manhajar X.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya kawo mafita ga yan Najeriya kan ƙoƙarin Tinubu na kawar da ƴan bindiga

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda ya yi magana a madadin Tinubu, ya bayyana fatansa game da farfado da tattalin arzikin Najeriya, tare da yin kira da a hada karfi da karfe domin ciyar da kasa gaba.

Ya bukaci masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin samun ci gaba, sannan ya yi alkawarin samar da makoma mai haske ga al’ummar kasa karkashin jagorancin Tinubu.

“Mu hada kanmu, mu taimaki shugaban mu. Daga nan zuwa Disamba, ina fata za mu sami dalilin da zamu yi murna. Mu hada kai domin kai al'ummar kasar nan zuwa tudun mun tsira," in ji Shettima.

Gwamna Diri ya naɗa kwamishinoni

A wani rahoton kuma Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP ya naɗa sababbin kwamishinoni 14 a gwamnatin jihar Bayelsa.

A wata takarda da ya rattaɓawa hannu, Gwamna Diri ya aike da sunayen waɗanda ya naɗa zuwa majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262