Ana Fargabar Mutane da Yawa Sun Mutu Yayin da Jirgin Sojoji Ya Jefa Bam a Filin Idi a Jihar Arewa
- Mazauna ƙauyen Kukawa a karamar hukumar Maradun a Zamfara sun yi ikirarin sojoji sun masu ruwan bama-bamai a filin idi ranar Laraba
- Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin ya zo wucewa sai ƴan bindiga suka buɗe masa wuta bisa haka ya saki bam ɗin da ya shafi fararen hula
- Amma mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji ya musanta labarin, inda ya ce ba shi da masaniya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Ana fargabar an kashe mutane da dama a kauyen Kukawa da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, yayin da sojoji suka kai farmaki ta sama.
Wani dan kauyen, Musa Abubakar wanda ya sha da kyar ya shaidawa jaridar Punch ranar Juma’a cewa suna cikin Sallar Idi ranar Laraba kwatsam sojojin sama suka yi ruwan bama-bamai a yankin.
Abubakar ya ce harin bama-baman sojojin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40 a ranar Ƙaramar Sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru
"Muna cikin sallar idi kawai muka hango jirgin yaƙin sojoji ya tunkaro wurin. Jirgin na ƙarisowa kwatsam muka ji kara mai ƙarfi, nan take kowa ya yi takansa.
"Ina daga cikin waɗanda suka taki sa'a suka tsira lafiya amma mutane da yawa sun mutu, wasu kuma sun samu raunuka. Na rasa mutane 13 a dangina," in ji shi.
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya ce jirgin sojojin ya saki ruwan bama-baman ne bayan wasu yan bindiga sun buɗe masa wuta.
Ya ce:
"Jirgin ya zo zai wuce ta ƙauyen kwatsam ƴan bindiga suka fara harbinsa, hakan ya sa sojoji suka jefa bama-bamai a kauyen ana tsaka da sallar idi, kuma mutane da yawa sun mutu."
Rundunar OPHD ta fayyace gaskiya
Da yake zantawa da jaridar ta wayar tarho, kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Laftanar Suleiman Omale, ya ce sojoji na yakar ‘yan bindiga ne ba fararen hula ba.
Ya kara da cewa ba shi da masaniyar an kashe wasu fararen hula da ba ruwansu yayin luguden wutar ta sama.
"Muna yakar ‘yan fashin daji ne, ba ‘yan Najeriya marasa laifi ba. Ba ni da masaniyar wani farar hula da aka kashe a yayin farmakin," in ji shi.
Farfesan jami'ar Sojoji ya rasu
A wani rahoton na daban jami'ar rundunar sojin Najeriya ta shiga jimami da alhini sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin manyan lakcarorinta.
Birgediya Janar Ali Williams Butu mai ritaya ya rasu yana da shekara 58 a duniya a wani asibitin kuɗi a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya.
Asali: Legit.ng