'Yan Najeriya Sun Yi Martani Kan Lafta Masu Haraji a Wani Titin Jihar Legas da Calabar

'Yan Najeriya Sun Yi Martani Kan Lafta Masu Haraji a Wani Titin Jihar Legas da Calabar

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da kudirin kafa shingen karbar haraji a kan sabuwar babbar hanyar Legas zuwa Calabar
  • Ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, ne ya bayar da sanarwar a wata hira da y ayi da 'yan jarida a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu
  • 'Yan Najeriya da dama na ci gaba da sukar kudirin ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana kudirin karbar Naira 3,000 a matsayin haraji kan kowacce kofar shiga da fice idan aka kammala babbar hanyar Legas zuwa Calabar.

Ministan ayyuka, Sanata Dave Umahi, ne ya tabbatar da wannan lamari a lokacin da yake hira da 'yan jarida.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Dave Umahi
Ministan ayyuka, Dave Umahi, ya ce gwamnati na son mayar da kudin da ta kashe ne cikin shekaru 15. Hoto: NTA Network News
Asali: Twitter

Adadin harajin da za'a rika karba

Ministan ya bayyana N3,000 a matsayin matsakaicin haraji da za a rinka karba. Amma ya ce akwai yiwuwar yin ragi wa kanan motoci su rinka biyan N1,500 sannan manyan motoci su rinka biyan N5,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, za a samar da tsaro a kofofin karbar harajin da kuma wasu wurare na musamman kamar gidajen mai.

Ya ce dalilin da yasa za a sanya harajin shi ne ana sa ran dawo da kudin da aka kashe wurin aikin hanyar ne cikin shekaru 15.

Biyo bayan kalaman nasa, 'yan Najeriya da dama sun mayar masa da martani, suna kokawa kan yadda gwamnatin tasu ke kara sa talakawa cikin tasko.

Wadanda suka soki tsarin

A cewar jaridar Vanguard, daga cikin wadanda suka yi fatali da matakin da gwamnatin ke shirin dauka akwai dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Hakazalika kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC): jam'iyyar Labour (LP); hadin gwiwar jam'iyyun siyasa (CUPP); kungiyar Niger-Delta (PANDEF) da masu aikin sufuri duk sun yi watsi da yunkurin gwamnatin.

Kwangilar hanyar Legas-Calabar

A wani rahoton kuma, kunji cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Tinubu da rufa-rufa wajen bayar da kwangilar babban titin Legas-Calabar

Gwamnatin tarayya ta bayar da kwangilar titin mai tsawon kilomita 700 ga kamfanin Hitech, kuma titin zai ratsa ta cikin jihohi tara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng