An Shiga Fargaba a Ribas Yayin da Aka Sace Dan Jaridar Channels TV, an Samu Sabbin Bayanai

An Shiga Fargaba a Ribas Yayin da Aka Sace Dan Jaridar Channels TV, an Samu Sabbin Bayanai

  • Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da dan jaridar Channels TV na jihar Ribas, Joshua Rogers a Fatakwal
  • An ce ‘yan bindigar sun tafi da wakilin gidan talabijin na Channels TV zuwa wani wuri da ba a san ko ina bane a daren ranar Alhamis
  • An ce Rogers yana kusa da gidansa da ke Rumuosi a Fatakwal, babban birnin jihar lokacin da ‘yan bindigar suka kai masa hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fatakwal, jihar Rivers - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani wakilin gidan talabijin na Channels TV a jihar Ribas, Mista Joshua Rogers.

An yi garkuwa da dan jarida a jihar Rivers
Rivers: Yan bindiga sun yi garkuwa da dan jaridan Channels TV bayan dawowa daga taro. Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Facebook

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Rogers a kusa da gidansa da ke Rumuosi a Fatakwal zuwa wani wuri da ba a san ko ina bane da misalin karfe 9 na daren ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a shingen binciken 'yan sanda, sun tafka babbar barna

Yadda aka sace dan jaridan Channels TV

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, dan jaridar yana tuka motarsa ​​ta kamfani mai dauke da sunan Channels Television a lokacin da ‘yan ta’addan suka tare shi, suka nuna masa bindiga tare da yin awon gaba da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce Rogers yana dawowa ne daga aikin da ya je yi a gidan gwamnati bayan zuwa wani taron gwamnati a Andoni lokacin da lamarin ya faru.

Tuni dai aka ce ‘yan bindigar sun tuntubi matarsa ​​inda suka bukaci a biya Naira miliyan 30 domin a sake shi, a cewar wani rahoto na SaharaReporters.

Wani mai daukarsa hoto ya tabbatar da faruwar lamarin tare da yin kira ga wadanda suka sace shi da su sako shi ba tare da wani sharadi ba.

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Bayan halartar taron aka sace dan jarida

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ya sake barkewa tsakanin Gwamna Fubara da magabacinsa, Nyesom Wike.

Gwamna Fubara, a wajen taron na ranar Alhamis, ya aike da gargadi ga shugabannin kananan hukumomin da ke yi masa rashin kunya a matsayinsa na gwamnan jihar.

Ebonyi: 'Yan bindiga sun kashe dan sanda

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun farmaki wasu 'yan sanda da ke binciken ababen hawa a Abakaliki, jihar Ebonyi kuma sun kashe jami'i daya.

An ruwaito cewa bayan kashe jami'in 'yan bindigar sun kuma kona motar sintirin 'yan sandan, kamar yadda kakakin rundunar na jihar Joshua Ukandu ya tabbatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.