Eid-El-Fitr: Jerin Gwamnonin Jihohin Arewa da Suka Ayyana Jumu'a a Matsayin Ranar Hutu
- Ma'aikatan gwamnati a wasu jihohi sun samu ƙarin lokacin da za su yi shagulgulan Ƙaramar Sallah tare da iyalansu
- Hakan ya faru ne saboda wasu gwamnonin Arewa sun bi sahun gwamnatin tarayya wajen tsawaita hutun Sallah zuwa Alhamis
- Legit Hausa ta tattaro muku jerin gwamnonin da suka yanke sanar da ƙara kwanakin hutun har zuwa ranar 12 ga watan Afrilu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwanan nan gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta tsawaita hutun bukukuwan Karamar Sallah zuwa ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.
Hakan ya biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu, inda ta bayyana hutun kwana biyu daga ranar Talata zuwa Laraba, 10 ga watan Afrilu.
Sai dai ba a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin ba, wanda hakan ya sa Sallar idi ta koma ranar Laraba. Bisa haka gwamnatin tarayya ta ƙara hutun kwana ɗaya watau ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar Tinubu, wasu gwamnoni a Najeriya sun tsawaita hutun Sallah ga ma'aikatan gwamnati zuwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024.
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin gwamnonin jihohin da suka ayyana ranar Jumu'a a matsayin ranar hutu ga ma'aikata.
1. Jihar Gombe
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya amince da ƙara kwanakin hutu zuwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, yayin da musulmi ke shagalin Ƙaramar Sallah.
A wata sanarwa da yammacin Laraba, Gwamna Yahaya ya ce ƙarin hutun zai ba mazauna jihar damar yin shagulgulan Sallah cikin jin dadi da nutsuwa.
Leadership ta tattaro cewa wannan ƙarin hutun ba zai rasa nasaba da cewa jihar Gombe ta saba yin hawan sallah na tsawon kwana uku karkashin Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar.
2. Jihar Katsina
Ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radɗa ya ayyana ranar Jumu'a a matsayin ranar hutun Ƙaramar Sallah.
Radda ya ce gwamnatinsa ta dauki wannan matakin ne domin baiwa ma’aikata a jihar damar yin shagalin Sallah tare da iyalansu, The Cable ta ruwaito.
Gwamna Raɗɗa ya kuma bukaci mazauna jihar da su yi taka tsan-tsan da sha'anin tsaro tare da addu'ar neman zaman lafiya a lokacin da suke murnar Sallah.
3. Jihar Sokoto
Haka zalika, gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Gwamna Ahmad Aliyu, ta ayyana Juma'a a matsayin ranar da babu aiki.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan, Abubakar Bawa, kuma ya rabawa manema labarai a jihar da yammacin ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.
Sanarwar ta kara da cewa an tsawaita hutun ne domin baiwa ma’aikatan jihar Sakkwato damar ci gaba da gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu.
Tsaro ya inganta a Katsina
A wani rahoton kuma Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa alamu sun nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in neman zaman lafiya da mutane suka yi a Ramadan.
Jim kaɗan bayan kammala sallar idi a Katsina, Gwamna Dikko ya ce tsaro ya kara inganta a faɗin jihar cikin ƴan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng