Babbar Kotu Ta Tsige Sarki Daga Karagar Mulki Bayan Gwamna Ya Amince da Naɗinsa

Babbar Kotu Ta Tsige Sarki Daga Karagar Mulki Bayan Gwamna Ya Amince da Naɗinsa

  • Babbar kotun jihar Osun ta soke naɗin Sarkin Ola, Oba Johnson Ajiboye, wanda Gwamna Ademola Adeleke ya naɗa a watan Janairu
  • Tun bayan karban mulki, Gwamna Adeleke ya soke wasu naɗe-naɗen sarakuna da magabacinsa ya yi, kana ya naɗa sababbi a yankuna daban-daban
  • Sai dai abin da ya faru a masarautar Ola ya zama rikici ne yayin da gidan da ke adawa da sabon sarkin suka shigar da ƙara a kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Rigingimu kan kujerar sarauta a garin Ola da ke yankin ƙaramar hukumar Ejigbo a jihar Osun sun ƙara tsanani yayin da kotu ta tsoma baki.

Babbar kotun jiha ƙarƙashin mai shari'a Lawrence Arojo ta tsige Oba Johnson Ajiboye, wanda Gwamna Ademola Adeleke ya naɗa a matsayin Sarkin Ola watau Olola na Ola.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnan Arewa ya faɗi alamun da ke nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in talakawa a Ramadan

Gwamna Ademola Adeleke na Osun
Sarkin da gwamna ya nada ya gamu da cikas a kotu Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Me ya kawo rikici a masarautar?

Jaridar The Nation ta gano cewa rikici ya ɓarke a yankin masarautar tun da Gwamna Adeleke, ranar 3 ga watan Janairu, ya sanar da naɗa Ajiboye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adeleke ya naɗa sabon sarkin ne a wani taron majalisar zartaswa ta jihar Osun duk kuwa da akwai ƙararraki kan masarautar a gaban kotu.

Shugaban masu ikon naɗa sarki a masarautar, Dakta Femi Fasanya, ya nesanta kansa tare da yin watsi da shirin nada Oba Johnson Ajiboye a watan Janairun 2024.

Bayan haka ne gidan da ke adawa Olugbode wanda David Salako da Kola Sangoniran suka wakilta, suka shigar da kara mai lamba HEJ/3/2020 a gaban babbar kotun.

Sun roƙi kotu ta kori Oba Johnson Ajiboye da kuma soke takardar nadin da Gwamna Adeleke ya ba shi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugabanci: An faɗi wanda ya cancanci zama sabon shugaban jam'iyyar PDP daga Arewa

Dalilin tsige Sarki a Osun?

Mai shari'a Arojo ya amince da bukatun cikin shari'a guda 6 da gida masu adawa suka gabatar a ranar 25 ga watan Maris, 2024 kan saɓawa doka.

Da take tsokaci kan lamarin, iyalan ta bakin lauyansu, Barista Fatimah Adeshina ta tabbatar da cewa kujerar Olola na Ola ta zama ba kowa bisa umarnin da babbar kotun jihar Osun ta bayar.

Sai dai da aka tuntubi Ajiboye, ya bayyana cewa, “Ni ne sahihin sarkin Ola, ba su kawo mun hukuncin da ya tsige ni daga sarauta ba."

Gwamnatin Jigawa ta fara bincike

A wani rahoton kuma Gwamnatin Jigawa a karkashin Gwamna Umar Namadi ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru a shirin ciyarwa na Ramadan.

Kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa, ya ce za a gudanar da bincike ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen shirin a karamar hukumar Babura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262