Gwamna Yusuf Ya Sake Nada Hadimin da Ya yi Barazana ga Rayuwar Alkalan Zaben Kano

Gwamna Yusuf Ya Sake Nada Hadimin da Ya yi Barazana ga Rayuwar Alkalan Zaben Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da mashawarcinsa kan matasa da wasanni Yusuf Shuaibu Imam kan mukaminsa bayan samunsa da kalaman tunzuri
  • Tun da farko, Gwamnan ya kori Ogan boye ne bayan ya yi kalaman tunzuri da barazana ga rayuwar alkalan dake sauraron shari’ar
  • A samarwar da mai Magana da yawun Gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce Ogan boye na daga wadanda su ka dawo kujerarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sake nada korarren hadiminsa Yusuf Shuaibu Imam a mukaminsa na mai bada shawara na musamman a bangaren matasa da wasanni.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan da aka tsige ya mayar da martani mai zafi, ya tona wani babban sirri

A wani rahoton daily trust, Gwamna Yusuf ya dakatar da Imam, wanda aka fi sani da Ogan boye bayan ya yi kalaman da ke barazana ga rayuwar alkalan da ke sauraron shari’ar gwamna Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.

Gwamna Yusuf ya dawo da Ogan boye mukaminsa
Ogan Boye: Hadimin Gwamnan Kano ya yi barazana ga rayuwar alkalan shari'ar zabe Hoto: Engr Abba Kabir
Asali: Facebook

Premium Times ta ce wadancan kalamai sun yamutsa hazo, wanda hakan ya tilastawa Gwamna Yusuf dakatar da Ogan boye da wasu yan jam’iyyar da su ka yi kalaman tunzuri ga al’umar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kano ta kori Ogan boye

Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantije ya sanar da korar Yusuf Shu’aibu Imam Ogan boye bayan ya yi kalaman tunzuri da kakkausan jawabi akan mataimaimakin shugaban kasa, Kashim Shettima lokacin da ake sauraron shari’ar gwamnan jihar, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ogan boye ya ce:

“ Duk Alkalin da ya bari aka yi amfani da shi wajen karbar cin hanci ya kuma fadi sakamako ba daidai ba, muna so mu fada masa sai dai ya zaba tsakanin rayuwarsa da kudin cin hancin da ya karba.”

Kara karanta wannan

"Za mu waiwayi bidiyon dala": Abba ya magantu kan shekara 8 na mulkin Ganduje a Kano

Abba ya yi wasu nade-naden a Kano

Ana da labari sauran wadanda aka nada su ne Farfesa Ibrahim Magaji Barde a matsayin mai bada shawara na musamman kan kudin shiga, Dr. AbdulHamid Danlado kuma a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasashen waje II.

A sanarwar da Sunusi Bature Dawakin Tofa, mai Magana da yawun Gwamna Yusuf ya fitar, an kuma nada Injiniya Bello Muhammad Kiru a matsayin mashawarci na musamman kan ruwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel