Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Ɓulla a Sakkwato, Ta Kashe Bayin Allah Kafin a Gano Lamarin

Annoba: Baƙuwar Cuta Ta Ɓulla a Sakkwato, Ta Kashe Bayin Allah Kafin a Gano Lamarin

  • Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta NCDC ta bayyana fargabar bullar wata bakuwar cuta a mazabun dake karamar hukum,ar Isan jihar Sakkwato
  • Yara masu karancin shekaru tsakanin 4-13 suka fi kamuwa da cutar da a yanzu haka ake fargabar ta kama mutane 164
  • Daga alamomin cutar akwai kumburin ciki, zazzabi, amai da rama, wanda tuni hukumar ta ce ta kafa kwamitin kar-ta-kwana domin lalubo bakin zaren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta tabbatar da ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Sokoto.

Hukumar ta ce ba a san asalin cutar ba, kuma zuwa yanzu mutane 4 sun rasu sakamakon cutar kamar yadda daily trust ta bayyana.

Kara karanta wannan

Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Ta'ammali Da Miyagun Kwayoyi Sama Da 300 A Kano

Hukumar NCDC ta bayyana cewa ana fargabar bullar bakuwar cuta a jihar Sakkwato
Bakuwar cutar dai ta fi kama yara tsakanin shekara 3-14 Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Darakta Janar na hukumar, Dr. Jide Idris ya ce zuwa yanzu, an ana zargin mutane 164 ne suka kamu da baƙuwar cutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Jide Idris ya kara da cewa:

"Mafi yawan masu kamuwa da cutar yara ne daga shekara 4-13, da kuma wasu manya. Marasa lafiyar sun zo daga mazaɓu daban-daban na ƙaramar hukumar."

Ana zargin an samu mutane ɗauke da baƙuwar cutar a ƙaramar hukumar Isa.

Mutanen da suka kamu da cutar a Sokoto

A cewar hukumar NCDC, mutane 22 daga mazaɓar Bargaja, da mutane 17 mazaɓar Isa ta Arewa, sai wasu mutum 98 daga Isa ta kudu ne ake zargin sun kamu da cutar.

Sauran mazaɓun da ake fargabar sun kamu da cutar sun fito daga mazaɓar Tozali (12), da Turba (11).

Wasu daga alamomin sun hada da kumburin ciki, zazzaɓi, amai, da rama, kamar yadda leadership ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

NCDC ta ɗauki matakin gaggawa

A cewar Darakta Janar ɗin, tuni suka ɗauki matakin kar-ta-kwana wajen shawo kan cutar tare da yin bincike.

Ya ce sun haɗa hannu da ma'aikatar lafiya ta jihar Sakkwaton domin lalubo bakin zaren.

An samu ɓullar cutar a 2023

Dr. Idris ya ce biyu daga wadanda ake zargi na dauke da makanciyar wannan cutar na samun kulawar kwararru a asibitin koyarwa na Usmanu Danfodiyo, UDUTH.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel