Ruwan Sama Ya Lalata Gine Gine Tare da Raba Mutane 3,000 da Gidajensu a Kogi

Ruwan Sama Ya Lalata Gine Gine Tare da Raba Mutane 3,000 da Gidajensu a Kogi

  • Guguguwar ruwan saman ta jefa mutane da dama cikin zulumi, musamman mata da kananan yara a jihar Kogi
  • Iftila'in ya mayar da magidanta da mata suna neman mafaka a gidajen makwabta da abokan arziki a wannan lokaci
  • An yi kira ga masu hanu da shuni, gwamnati da kungiyoyin sa kai da su tallafawa wadanda abin ya afkawa don rage musu radadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Guguwar ruwan sama ta yi barna a unguwar Iyara hedikwatar karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.

Guguwar ta kwashe rufin gidaje sama da guda 100 yayin da sama da mutane 3,000 suka rasa gidajensu.

Kara karanta wannan

FCTA: Wike ya kaddamar da rusa gidajen mutane a Abuja, bayanan rusau sun fito

Gidajen da guguwar ruwan sama ta lalata
Guguwar ruwan saman ta faru ne unguwar Iyara a karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi. Hoto: Leadership. Asali: Facebook
Asali: Facebook

Ruwa ya jawo mutane sun rasa gidaje

Guguwar ruwan sama dai ta auku ne a daren Litinin din da ta gabata kuma yanzu haka mazauna yankin suna cikin zaman zulumi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon rasa muhallan nasu, wasu daga cikinsu sun nemi mafaka a gidajen 'yan uwa, makwabta da abokan arziki.

Kogi: Halin da Bayin Allah suke ciki

Da yake jawabi jim kadan bayan ziyartar wurin da iftila'i ya faru, basaraken yankin, Oba Jacob Meduteni, ya bayyana hadarin a matsayin babban abin bakin ciki.

Ya kara da cewa jarrabawa ce babba musamman a daidai lokacin da jama’a ke cikin halin kunci da matsin tattalin arziki, Tribune Online ta ruwaito.

Mata da yara sun fi shiga matsi

A nasa bangaren, shugaban kungiyar cigaban Iyara ta kasa, Alhaji Aliyu Badaki, ya ce bala'in ya shafi sama da mutane 1,000 wadanda galibinsu mata ne da kananan yara.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Alhaji Badaki ya bayyana barnar da guguwar ta yi a matsayin babba, kuma yace bala'i ne da ya wuce wadanda abin ya shafa su dauka su kadai musamman idan aka lura da yanayin tattalin arzikin da kasar ke ciki.

Bukatar neman taimako a Kogi

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa basaraken garin, Oba Meduteni, ya yi kira ga attajirai da kungiyoyin sa kai da su taimaka wa wadanda abin ya shafa don rage musu radadin da suke ciki.

Haka zalika shima Alhaji Badaki yayi kira ga gwamnatin jihar Kogi ta hannun hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, SEMA, da kuma gwamnatin tarayya ta hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), da su kawo agajin gaggawa ga wadanda abin ya shafa.

Kamaru ta sako ruwa, 'yan Najeriya su shirya, inji NEMA

A shekarar da ta gabata ne hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta samu sanarwar ankara kan ambaliyar ruwa a gabar kogin Benue.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Ma'aikatar harkokin wajen kasar nan ne ta fitar da sanarwar a wata wasikar da TheCable ta gani, mai kwanan wata 21 ga watan Agusta.

Ana yawan samun ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya, musamman duba da yadda ake cike magunanan ruwan sama da datti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng