InnalilLahi: Ƴan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro 30 Ana Shirin Ƙaramar Sallah a Arewa

InnalilLahi: Ƴan Bindiga Sun Halaka Jami'an Tsaro 30 Ana Shirin Ƙaramar Sallah a Arewa

  • Wasu ƴan bindiga sun yi ajalin dakarun rundunar ƴan sa'kai 30 yayin wata musayar wuta a ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja
  • Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Garba, ya tabbatar da kashe jami'an tsaron ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024
  • Ya kuma bayyana damuwa kan yadda ƴan bindiga ke yawan kai hare-hare kan manoma yayin da ake shirye-shiryen zuwan damina

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Wasu ƴan bindiga da ke yawan kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar Mariga a juhar Neja sun kashe jami'an rundunar ƴan sa'kai 30.

An kafa rundunar ƴan sa'kai a jihar da ke Arewa ta Tsakiya ne domin su yaƙi ƴan bindiga tare da haɗin guiwar hukumomin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, sun tafka ɓarna a jihar Arewa

Yan sanda.
Yan bindiga sun kashe yan sa'kai da yawa a Neja Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa ƴan bindigar sun kashe ƴan sa'kai 30 a yankin ƙauyen Dogon Giwa yayin wani artabu da ya gudana a tsakaninsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024.

Ya kuma nuna matuƙar damuwarsa kan yadda ƴan bindigar ke yadda suka ga dama ba tare da an taka masu birki ba, suna farmakar manoma yayin da ake tunkarar damina.

Ciyaman ya roƙi gwamnati

Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma yi kira ga gwamnati ta kawo masu ɗauki tare da gudanar da bincike kan kisan waɗannan bayin Allah, The Nation ta ruwaito.

Yayin da aka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, domin jin ta bakinsa ba a same shi ba har zuwa lokacin haɗa rahoton.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun dira sansanin manyan ƴan bindiga 3 a Arewa, sun kashe da yawa ranar Sallah

Legit Hausa ta fahimci cewa Neja na ɗaya ɗaga cikin jihohin Arewacin Najeriya da hare-haren ƴan bindiga suka yi wa illa.

Gwamnatin Neja ta bada umaenin harbi

A wani rahoton na daban Gwamnatin jihar Neja ta amince da jami'an tsaro su harbe duk dan dabar da su ka gani yawo da muggan makamai a jihar

An dauki matakin ne a tarom masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262